Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta kasa (JAMB) ta dakatar da gudanar da rijistar DE ta shekarar 2023, wacce aka fara a ranar Litinin, 20 ga watan Fabrairu, 2023.
Dakatarwar, a cewar sanarwar da Dakta Fabian Benjamin, shugaban sashen hulda da jama’a da kuma ka’idojin hukumar ta JAMB ya fitar a ranar Talata, yace an yi ta ne domin a ba da damar aiwatar da wasu tsaruka, wadanda aka tsara don kyautatawa masu son yin rajistar.
Idan dai ba a manta ba Hukumar ta fara rajistar DE ne a ranar Litinin 20 ga Fabrairu, 2023, zuwa ranar Alhamis 20 ga Afrilu, 2023.