Hukumar shirya jarabawar shiga makarantun gaba da sakandire ta JAMB, ta sanar da rage kudin rajistar jarrabawar shiga manyan makarantun gaba da sakandire (UTME) daga naira 5,000 zuwa naira 3,500 ga masu fama da bukata ta musamman.
Wannan yunƙurin an yi shi ne da nufin karfafa wa masu bukata ta musamman (PWD) gwiwar ci gaba da karatu zuwa manyan Makarantu.
- PDP: Gwamnan Bala Ya Kalubalanci Wike Kan Kunno Wutar Rikicin Jam’iyya A Bauchi
- Ambaliya: A Hada Gwiwa Don Ceto Borno – Gwamnatin Kano
Magatakardar JAMB, Ishaq Oloyede ne ya bayyana hakan a lokacin da yake ganawa da manema labarai ranar Litinin a Abuja.
Oloyede ya jaddada mahimmancin bayar da dama iri daya ga kowa domin samun ingantaccen Ilimi, yana mai cewa, “Kungiyar JAMB’s Equal Opportunity Group (JEOG) za ta gudanar da taronta na farko na yankin Afirka kan daidaiton damar samun ilimi mai zurfi (ARCEAHED) don haɓaka damar samun ilimi mai zurfi ga masu bukata ta musamman a manyan makarantu a fadin Afirka.”
Taron zai samu halartar mahalarta daga kasashe da suka hada da Habasha, Malawi, da Masar.
Taron za a yi shi ne a ranakun 17-18 ga watan Satumba, 2024 a dakin taro na Idris Abdulkadir da ke cibiyar NUC, Maitama Abuja.