Jami’an kasa da kasa sun dora muhimmanci sosai kan babban bikin tunawa da cika shekaru 80 da samun nasarar yakin da al’ummar Sin suka yi da mamayar dakarun kasar Japan, da yakin kin tafarkin murdiya. Kuma sun bayyana cewa, muhimmin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi a yayin bikin, ya jaddada cewa, kasarsa na tsayawa kan tafarkin samun ci gaba cikin lumana, kuma hakan ya kara wa kasashen duniya imani da kwarin gwiwar koyon darasi daga tarihi, da hada kai don inganta zaman lafiya da ci gaban dan Adam.
Mataimaki na farko ga shugaban majalisar dokokin Duma ta kasar Rasha, kuma shugaban majalisar sada zumunci tsakanin kasashen Rasha da Sin Ivan Melnikov ya bayyana cewa, shugabannin kasa da kasa mahalarta bikin, dukkansu suna goyon bayan bin hanyar hadin kai, da gudanar da hadin gwiwa bisa daidaito da adalci, kuma hakan dai dace da ruhin sanarwar Tianjin da aka fitar a kwanan baya.
A nasa bangaren, mataimakin shugaban kwamitin tsaron kasa na majalisar dokokin kasar Slovakia Michal Bartek ya ce, jama’ar kasar Sin na da tsayayyen matsayin adalci na tarihi, da ci gaban wayewar kan dan Adam, don haka, ya amince da jawabin shugaba Xi sosai. A cewarsa, abun da ya fi muhimmanci shi ne, kasar Sin na amfani da makamai ne don tabbatar da zaman lafiya a nan gaba, maimakon kai hari kan sauran kasashe.
Shugaban jam’iyyar Hungarian Workers’ Party ta kasar Hungary Thurmer Gyula ya bayyana cewa, sassan kasa da kasa sun gano manyan nasarorin ci gaba da Sin ta samu a fannonin aikin soji, da tattalin arziki da dai sauransu, a waje guda kuma, sun gano fatan kasar na yin hadin kai tare da kasashe daban daban don samun nasara tare. (Bilkisu Xin)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp