Kakakin maaikatar kasuwancin kasar Sin Shu Jueting ta bayyana a jiya Alhamis cewa, jamian cinikayya na kasar Sin da Amurka sun jaddada muhimmancin dangantakar tattalin arziki da cinikayya tsakanin kasashen biyu, kuma sun amince su kiyaye da karfafa muamalarsu.
Ministan kasuwanci na kasar Sin Wang Wentao ya gana da sakatariyar kasuwancin Amurka Gina Raimondo da kuma wakiliyar cinikayyar Amurka Katherine Tai a makon da ya gabata a lokacin da ya kai ziyara Amurka domin halartar taron ministocin kasuwanci na kungiyar APEC.
Bangarorin biyu sun yi musayar raayi kan batutuwan da suka shafi tattalin arziki da cinikayya, tare da tattauna batutuwan da suka shafi hadin gwiwa, in ji Shu a yayin taron manema labarai.
Kasar Sin tana fatan kasar Amurka za ta yi aiki tare da kasar Sin wajen tafiyar da bambance-bambance, da kiyayewa da zurfafa hadin gwiwa a fannin tattalin arziki da cinikayya cikin adalci, bisa kaidojin mutunta juna, da zaman lafiya, da yin hadin gwiwa don cimma nasara tare, ta yadda za a samu moriyar kasashen biyu da jamaarsu, da kuma inganta ci gaban tattalin arzikin duniya, in ji Shu. (Mai fassarawa: Yahaya)