Jami’an tsaron hadin vuiwa da wasu ‘yan sintiri sun yi nasarar halaka wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne guda 21 a karamar hukumar Danko Wasagu a jihar Kebbi.
Shugaban karamar hukumar, Alhaji Hussani Aliyu-Bena, ya bayyana cewa, jami’an sun yi wannan nasarar ne a ranar Laraba.
- Harin ‘Yan Bindiga A Kauyen Dan-Umaru: ‘Yansanda Sun Kwato Roka A Kebbi
- ‘Yansanda Sun Kashe ‘Yan Bindiga 4 Tare Da Cafke 9 A Jihar Kaduna.
A cewarsa, an kashe su ne a lokacin da suke shirin tsallaka wa jihar Kebbi, ta hanyar da ta taso daga yankin Mariga da ke a jihar Neja, inda jami’an suka yi masu kwanton bauna a yankin Tudun Bichi suka kuma samu nasarar hallaka su.
Shugaban ya ci gaba da cewa, Wasagu ta yi iyaka ne da Mariga da ke a jihar Neja wadda ta zamo wa ‘yan bindigar hanya mafi sauki da suke yin amfani da ita don shiga cikin yankunan da ke cikin jihar Kebbi.
Kazalika, ya bayyana cewa, ‘yan bindigar sun kuma kashe Marafan Mai Inuwa, da ke a karkashin gundumar Kanya tare da sace wasu mutane, amma daga baya, soji suka ceto su, suka kashe wasu daga cikin ‘yan bindigar.
Ya bukaci da a kara tura yawan jami’an tsaro zuwa yankunan Malekachi da Dankade, ganin cewa, ‘yan bindigar na yin amfani da hanyoyin wadannan yankunan don wucewa.
Shugaban, ya yabawa jami’ai kan wannan namijin kokarin na halaka ‘yan bindigar.
A cewars, bisa umarnin gwamanan jihar, Nasiru Idris, ‘yan majalisar karamar hukumar sun kai ziyara gundumar ta Kanya, wajen da alummar da ‘yan bindiga suka raba su da matsagunansu suka taru a nan.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoton, Kakakin rundunar ‘Yansandan jihar, SP Nafiu Abubakar, bai fitar da wata sanarwa kan wannab lamarin ba.