Jami’an tsaro a jihar Kebbi sun sami nasarar dakile harin ‘yan ta’addar Lakurawa da suka kai a kauyen Malan Yaro, karamar hukumar Dandi.
Lamarin ya faru ne a ranar 25 ga Nuwamba 2025 da misalin karfe 5:26 na safe, lokacin da wasu mutane dauke da makamai da ake kyautata zaton ‘yan kungiyar ta’addanci ta Lakurawa ne da suka mamaye yankin suka kaddamar.
- Peng Liyuan Ta Halarci Aikin Fadakarwa Albarkacin “Ranar Cutar Sida Ta Duniya” Ta 2025
- Gwamnatin Kano Ta Fara Ɗaukar Matakan Daƙile Dawowar Masu Achaba
A cewar wata sanarwa da jami’in hulda da jama’a na ‘yansanda, CSP Nafiu Abubakar Kotarkoshi, ta ce, jami’in ‘yansanda na yankin Kamba ne ya jagoranci tawagar ‘yansanda da ‘yan banga zuwa wurin.
Tawagar tsaro ta bi maharan an kuma yi musayar wuta da su a wani mummunan faɗa da ya ɗauki tsawon awanni ana fafatawa.
“An kashe ɗaya daga cikin ‘yan bindigar, yayin da wasu suka tsere cikin daji bayan sun samu raunukan harbin bindiga. An gano babura biyu da wadanda ake zargin suka gudu suka bari,” in ji sanarwar.














