Jami’an tsaro a Jihar Kwara sun kashe ƙasurgumin mai garkuwa da mutane, Maidawa, tare da wasu daga cikin ‘yan tawagarsa a wani samame da suka kai kusa da Isanlu-Isin.
Wata majiya daga jami’an tsaro ta bayyana cewa an gudanar da aikin ne a ranar 30 ga watan Satumba, 2025, a ci gaba da yunƙurin kawar da masu garkuwa da mutane a jihar.
- Gwamnatin Tarayya Ta Yi Gargaɗi Kan Yiwuwar Aukuwar Ambaliya A Wasu Jihohi
- PSG Ta Doke Barcelona Har Gida A Gasar Zakarun Turai
Majiyar ta ce labarin mutuwar Maidawa ya isa ga sauran ‘yan ƙungiyar ta hannun wani ƙasurgumin mai garkuwa da ake nema, Baccujo, wanda ya tattauna da abokan aikinsa a Katsina.
Ta ƙara da cewa kiraye-kirayen da gwamnatin jihar ta yi na neman gaggawar ɗaukar mataki ya sa jami’an tsaro suka ƙara ƙaimi wajen fatattakar masu garkuwa da mutane, waɗanda ke kai wa ƙauyuka hare-hare kuma suna yin garkuwa da mutane domin karɓar kuɗin fansa.
An gudanar da ayyukan ne a matakai daban-daban a wuraren da aka fi garkuwa da mutane a ‘yan makonnin nan, ciki har da Ekiti, Ifelodun, Isin, Edu da Patigi.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp