Jami’ar Jihar Kwara (KWASU) ta sanar da rage Naira 100,000 na kudin makaranta ga dalibai masu bukata ta musamman.
Mataimakin shugaban jami’ar, Farfesa Shaykh-Luqman Jimoh ne ya sanar da hakan a wata sanarwa da mukaddashin daraktar hulda da jami’ar, Dr. Saidat Aliyu ta fitar.
- Kwamitin Kolin JKS Ya Gudanar Da Taron Tattaunawa Don Neman Shawarwari Kan Aikin Tattalin Arziki
- Gwamnan Zamfara Ya Rantsar Da Sabon Kwamishina Tare Da Yin Garambawul Ga Muƙarrabansa
Hakazalika, ya ce jami’ar tana aiwatar da tallafin Naira 50,000 kowane wata ga ma’aikatan jami’ar masu fama da bukata ta musamman tare da ƙarin guraben aikin yi ga masa a fannin koyarwa na masu bukata ta musamman.
Jimoh ya bayyana hakan ne yayin da yake magana a wani taron da aka shirya don bikin ranar masu bukata ta musamman ta duniya ta 2024 a ofishin tallafawa nakasassu na jami’ar da ke Sashen Ilimi na Musamman.