Jakadar kasar Falsdinu a Masar ya mika godiyar kasarsa ga gwamnatin kasar Sin da jama’arta bisa yadda suka samar da kayayyakin jin kai a kan lokaci zuwa zirin Gaza da rikici ya dabaibaye.
Dial al Louh ya bayyana hakan ne a yayin wani bikin nuna godiya ga kasar Sin bisa taimakon da take bayarwa wanda ya gudana a ranar Lahadi a birnin Alkahira na kasar Masar, wanda ya samu halarcin jakadan kasar Sin a Masar Liao Liqiang da babban daraktan kungiyar ba da agaji ta Red Crescent ta Masar Rami Al-Nazer.
- Xi Ya Bukaci A Tsagaita Bude Wuta Tare Da Gudanar Da Tattaunawar Zaman Lafiya Kan Rikicin Falasdinu Da Isra’ila
- Xi Jinping Ya Aike Da Wasikar Taya Murna Ga Taron Kasa Da Kasa Na Congdu Na 2023
Ya kuma mika godiya da girmamawa na mahukuntar Falasdinawa da al’ummar Falasdinu ga kasar Sin bisa taimakon da take bayarwa a lokutan da al’ummar Gaza ke cikin bala’in jin kai.
A nasa bangaren, Al-Nazer ya ce, bangaren Masar ya yaba da yadda kasar Sin ke ba da agajin jin kai a zirin Gaza, kuma za ta ci gaba da ba da taimako wajen shigar da kayayyaki da rarraba kayayyakin. (Muhammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp