Wani jami’in kiwon lafiya na kasar Morocco, ya yaba da gudummawar da kasar Sin ta bayar wajen inganta harkokin kiwon lafiyar kasar a cikin shekaru sama da goma da suka gabata, ta hanyar tura tawagar likitocin kasar Sin zuwa kasar dake yankin arewacin Afirka.
A yayin wata zantawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua na kasar Sin a baya-bayan nan, daraktan sashen tsare-tsare da albarkatun kudi na ma’aikatar lafiya da kare jin dadin jama’a ta kasar Morocco, Belmadani Abdelwahab ya jaddada muhimmancin karfafa alakar dake tsakanin Morocco da kasar Sin a fannin kiwon lafiya.
Tun lokacin da tawagar farko ta likitocin kasar Sin ta isa Morocco a shekarar 1975, ya zuwa yanzu kasar Sin ta aike da jami’an kiwon lafiya kusan dubu biyu, a cikin rukunoni 195 zuwa kasar. Ya zuwa yanzu sun ba da hidimomin kiwon lafiya kyauta ga kusan majinyatan Morocco miliyan 5.78, baya ga aikin tiyata kusan duba 530 da suka gabata. (Mai fassarawa: Ibrahim)