Jami’o’i 67 a Nijeriya, sun yaye dalibai 6,464 masu daraja ta daya cikin shekaru uku daga fannonin ilimi daban-daban.
Haka zalika, masu ruwa da tsaki sun bukaci a rika samar da isassun kudade tare da mayar da hankali wajen koyar da ilimin sana’oi.
- Masana Sun Yabawa Rawar Da Sin Ke Takawa Wajen Inganta Ilimi A Afrika
- An Yi Kira Da Aiwatar Da Matakan Samar Da Ilimi Mai Inganci A Nahiyar Afirka
Duk da cewa, ana ta faman korafe-korafe a kan rashin isassun kudaden tafiyar da Jami’oi da rashin isassun kayan aiki da rashin isassun malamai da yawan tafiya yajin aiki da rashin ingantaccen bincike da rashin iya gudanar da mulki da tabarbarewar tsaro tare kuma da yadda wasu ke barin aikin koyarwa, suna komawa wasu wuraren da ake kulawa da hakkokinsu fiye da wuraren da suka bari.
Har ila yau, Jami’oin Nijeriya sun ci gaba da yaye dalibai, wadanda suka samu digiri mai daraja ta daya da yawan gaske daga kuma fannoni daban-daban.
Wannan al’amari, na tafiya ne kamar yadda aka saba yi a shekarun baya, ta yadda Jami’oi kalilan ne ke iya yaye dalibai da irin wannan sakamako, su ma din sai masu kyan gaske ne daliban kan samu wannan sakamako mai daraja ta daya.
Sannan, Yawan yajin aikin da kungiyar malaman jami’oi ke yi tsawon lokaci, an danganta shi da rashin mayar da hankali a kan koyar daliban, hakan yasa kungiyar ta nuna cewa, a cikin irin wannan yanayi na karatu; ko kadan bai dace jami’oin su rika samar da daliban da za su samu irin wannan digiri mai daraja ta daya ba, kamar yadda wasu jami’oin da suka amsa sunansu suke samarwa ba.
Duk da irin halin ko matsalolin da jami’oin ke fuskanta, amma sai ga shi suna yaye irin wadannan dalibai wadanda suka fi taka rawar gani a jarabawar kammala jami’a.
Binciken da LEADERSHIP ta yi ya nuna cewa, jami’oi 67 daga cikin 272; wadanda suka yi bikin yaye dalibansu ko na wadanda suka kammala karatunsu tare da wadanda suka riga su kammalawa a tsakanin watan Maris na 2023 zuwa 2024, an samu dalibai 6,464 da suka samu digiri mai daraja ta daya.
Kazalika, an samu wadannan alkaluma ne daga jawabin ranar bikin yaye dalibai na Mataimakan Shugabannin Jami’oin da kuma sauran masu ruwa da tsaki na wadannan jami’oi.
Jami’o’in Gwamnatin Tarayya, su ne kan gaba; inda suka yaye dalibai 3,736, wato kashi 57.79 cikin 100, na masu digiri mai daraja ta daya, sai kuma jami’o’i mallakar gwamnatocin jihohi da suke da dalibai 1,458, kashi 22.55 cikin 100, yayin da kuma jami’oi masu zaman kansu ke da dalibai 1,270 , kashi 19.64 cikin 1oo, na yawan wadannan dalibai cikin shekaru uku kacal.
Don haka, idan aka duba za a tarar cewa, Jami’oin Gwamnatin Tarayya 23, su ne kan gaba na wadanda suka samu wannan digiri mai daraja ta daya da dalibai 3,736, sannan, jami’oin jihohi 18 ke biye da su da dalibai 1,458, su kuma jami’oi masu zaman kansu 26, ke da dalibai 1,270.
Bugu da kari, binciken LEADERSHIP ya kara nuna Jami’ar Ilori da ke Jihar Kwara, ita ce kan gaba na wadanda suka kammala wannan digiri mai daraja ta daya da dalibai 450, Jami’ar Jihar Legas a matsayin ta biyu da 340, Jami’ar Abubakar Tafawa Balewa da ke Bauchi da dalibai 337, Jami’ar Ibadan da dalibai 314; Jami’ar Nijeriya ta Nsukka da dalibai 288; Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Akure da ke Jihar Ondo da dalibai 195; Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Minna da dalibai 187; Jami’ar Ahmadu Bello Zariya da dalibai 182; Jami’ar Bayero ta Kano da dalibai 180; Jami’ar Benin da dalibai 178, Jami’ar Obafemi Awolowo Ile-Ife da ke Jihar Osun da dalibai 158.
A banagaren jami’oi mallakar jihohi kuma ta Jihar Legas ce kan gaba da dalibai 282; mai bi mata kuma ita ce, Jami’ar Olabisi Onabanjo Ago Iwoye ta Jihar Ogun da dalibai 198; Jami’ar Jihar Kwara Malete da dalibai 183, Jami’ar Jihar Gombe kuma na da 116.
Har wa yau, jami’oi masu zaman kansu kuma, Jami’ar Cobenant da ke Ota a Jihar Ogun, na da yawan dalibai 283, Jami’ar Afe Babalola Ado Ekiti ta Jihar Ekiti na da dalibai 141; Jami’ar Fountain, Osogbo a Jihar Osun, na da dalibai 89; Jami’ar Bowen Iwo a Jihar Osun, na da dalibai 82, sai kuma Jami’ar Landmar Omu-Aran, a Jihar Kwara ked a dalibai 68.
A yawan alkaluman da LEADERSHIP ta bayyana, Jami’ar Abuja ta samar da masu digiri na daya da dalibai 152 daga cikin dalibai 8,144 da suka kammala nasu karatun.