Manyan Jami’o’in kasashen Sin da Najeriya, sun yi kira da a karfafa fahimtar juna tsakanin al’adun mabanbantan sassa, musamman na kasashe masu tasowa, tare da yin hadin gwiwa don yaukaka zaman lumana, da wayewar kai mai kunshe da makomar bai daya ga dukkanin bil adama.
Yayin wani dandali mai taken “Musayar wayewar kai da koyi da juna tsakanin Sin da Najeriya”, wanda ya gudana a ranar Juma’a, mahalarta sun tattauna game da bukatar ingiza shawarwari da fahimtar juna tsakanin Sin da Najeriya.
- Zargin Kwacen Waya: Fusatattun Matasa Sun Bankawa Keken Adaidaita Sahu Wuta A Kano
- Maryam CTV Ta Nemi A Dinga Nuna Al’adun Bahaushe Maimakon Na Wasu Kasashen Waje A Fina-finan Kannywood
Da yake tsokaci game da hakan, shugaban tsangayar koyar da ilimin kimiyyar siyasa da alakar kasa da kasa a jami’ar birnin Abuja fadar mulkin Najeriya, Dakta Sheriff Ghali Ibrahim ya ce “A ganinmu, al’umma guda ita kadai tana da nakasu, har sai an yi musayar kwarewa, da koyi da juna tsakanin mabanbantan wayewar kai”.
Shi ma a nasa tsokaci yayin gudanar da dandalin, jakadan Sin a Najeriya Yu Dunhai, ya yi karin haske game da rawar da dandalin ke takawa, wajen yaukaka musayar al’adu da koyi da juna tsakanin Sin da Najeriya. Yana mai jaddada aniyar kasar Sin ta yin aiki tare da Najeriya, wajen ingiza manufar wayewar kai tsakanin sassan kasa da kasa a Najeriya.
Sashen koyar da ilimin aikin jarida da sadarwa na jami’ar Tsinghua ta kasar Sin, da tsangayar koyar da ilimin kimiyyar siyasa da alakar kasa da kasa na jami’ar birnin Abuja ne suka shirya dandalin. (Saminu Alhassan)