Zuwa yanzu daga dakin tattara sakamakon Zaɓen Shugaban Kasa da ake a Kano, Jam’iyyar NNPP wadda Tsohon Gwamnan Jihar Kano Kuma Tsohon Sanatan Kano ta tsakiya Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso kewa takarar Shugabancin Kasa shi ne ke Kan gaba Inda Jam’iyyar tasa ta NNPP Ta lashe Kananan Hukumomin
Warawa, Gabasawa, Minjibir, Gezawa, Kibiya, Rimin Gado Makoda da Garun Malam.
Wannan sakamakon na kara tayarwa da Jam’iyya Mai mulki hankali dake ganin kamar hakan ba zai yiwu ba, duk da cewa an samu ‘yan matsalolin a wasu yankuna, inda ake Zargin Kama wasu Jami’an wata Jam’iyya Sanye da kayan Hukumar zabe, Haka ma a Karamar Hukumar Takai an samu yamutsa gashin Baki tare da jikkata wasu mutane.
Labarin da muke samu daga abokan aikinmu dake wajen dakin taron na bayyana cewa kusan zuwa yanzu akwai yiwuwar wakilin Gaya, Jingi da Albasu, Nasarawa, Tarauni ana zaton an kaisu Kasa, shima Sanatan Kano ta tsakiya, da Sanatan Kano Kudu dukkansun ana ganin suna cikin damuwa kwarai nayin bakwana da kujerunsu.