Babbar Jam’iyyar adawa a Nijeriya, (PDP) ta ci alwashin ɗaukar matakin da ya dace kan tsohon Gwamnan Ribas kuma Ministan Abuja, Nyesom Wike da wasu ‘yan jam’iyyar bisa zargin yi mata zagon ƙasa.
Majalisar ƙoli ta jam’iyyar PDP mai adawa a Nijeriya ta ce za ta ɗauki matakan ladabtarwa kan Miinistan Abujan, Nyesom Wike, da wasu ‘yan jam’iyyar.
Shugaban jam’iyyar PDP na ƙasa, Umar Damagum, ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai ranar Talata. Jam’iyyar tana mai ikirarin cewa ta sha bamban da matsayar da Shugaba Tinubu ya ɗauka kan rikicin siyasar ta jihar Ribas.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp