Gwamna Ahmadu Umaru Fintiri, ya jaddada bukatar samun hadinkan jama’a da bangarorin jam’iyyu da ‘yan siyasar jihar domin bashi damar samun gina jihar Adamawa.
Fintiri, ya bayyana haka ne a wani taron gagarumin tarban da jama’a magoya baya suka shirya masa ranar Juma’a, lokacin da ya dawo Yola fadar jihar tun bayan da kotun Koli ta ayyanashi a matsayin halastaccen gwamna.
- Hukuncin Zaben Adamawa: Na Rungumi Kaddara – BinanBinani
- Kotun Koli Za Ta Saurari Shari’ar Zaben Gwamnan Adamawa A Ranar Litinin
Gwamna Umaru Fintiri, ya ci gaba da cewa “gwamnatina ba zata bada damar gudanar da wargi da hayaniya ko hamayya irin na siyasa marar ma’ana ba, kuma ba zai yi kasa a gwiwa ba wajen ganin an samar da tsarin dimokuradiyya ga kowane dan jihar.
“A ko da yaushe gwamnatina na kan gaba wajen tafiyar da al’umma, ba tare da la’akari da matsayar da suke kanta ko jam’iyyarsu ba, ina kira ga ‘yan jiha da su bamu goyon baya don gina jihar da suke so da kuma burin ganin ta ci gaba.
“Ba mu taba haifar cece-koce ko wani gibi a shugabanci ba, a ko da yaushe muna tabbatar wa al’ummar jiha cewa za mu yi musu aiki, da kuma yi musu abinda ya kamata, ba mu taba shagaltuwa ko na dakika guda ko domin hayaniyar ’yan siyasa kan da nauyin dake kanmu ba” inji Fintiri.
Da yake magana kan hukuncin kotun koli kuwa, gwamnan ya yabawa bangaren shari’ar, ya kara da cewa “hukuncin kotun ya zaburar dani wajen kara gwazo, zanyi iyakacin kokarina da tsayawa tsayin daka da kuma tabbatar da cewa an yi adalci ga jama’a.
“Ban taba rasa imani da bangaren shari’a ba, na fadi lokacin babu adadi, sun tsaya tsayin daka su na gudanar da aikinsu yadda ya dace, hukunce-hukuncensu bai kasance cikin rudani kamar yadda Hudu Ari ya yi wa hukumar zabe INEC ba.
“Don haka zan ci gaba da hadakai da bangaren shari’a domin mu gina dimokuradiyya da gina jiha da kasarmu” inji Fintiri.