Har yanzu, Nijeriya na ci gaba da mafarkin samun jajirtancen shugaban kasa na gari; mai kuma kishin kasa tamkar Janar Murtala Ramat Muhammed.
Wannan dalili ne ya sanya, a kowane lokaci irin wannan ake ci gaba da aiwatar da bukukuwan tunawa da shi tare da mararinsa; sakamakon irin gudunmawa da kuma sadaukar da rayuwarsa da ya yi, don ci gaban wannan kasa.
- Kauyuka Suna Kokarin Neman Cimma Burin Samun Wadata Tare A Kasar Sin
- Kar Ku Tayar Da Hankalinku Kan Cutar Tsuntsaye – Ma’aikatar Lafiya Ta Kano
Kamar yadda tarihi ya nuna, an haifi marigayi Janar Murtala Ramat Muhammed, ranar 8 ga watan Nuwambar shekara ta 1938 a garin Kano.
Har ila yau, ya yi karatun firamarensa a Jihar Kano; inda kuma ya yi na sakandirensa a Kwalejin Barewa da ke garin Zariya. Sannan, a shekarar 1959 ne ya shiga aikin soja, kazalika; ya yi karatu a makarantar sojoji ta ‘Royal Military Academy’ ta Sandhurst da ke Kasar Burtaniya.
Bugu da kari, Janar Murtala ya samu nasarar samun mukamin Laftanal a shekarar 1961. Haka zalika, kafin komawarsa Nijeriya a shekara ta 1962, ya je rangadin aiki a Kasar Kongo; a matsayin wakilin dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya.
A shekarar 1964 ne kuma, aka ba shi mukamin Manjo na wucin gadi, bayan ba shi ragamar kula da sashen sadarwa a Hedikwatar Rundunar Soji ta Kaduna.
Har wa yau, Ramat ya koma Jihar Legas; inda ya zauna tare da kawunsa, Alhaji Inuwa Wada; a daidai lokacin da aka nada shi Ministan Tsaro, sannan ya ci gaba da kasancewa a can; har zuwa lokacin da aka yi juyin mulki na farko a shekarar 1966.
Tun bayan wannan juyin mulki na farko ne, Janar Murtala ya rika neman yadda zai hada kan sojojin Arewa da ke Jihar Legas; domin sake yin juyin mulki a karo na biyu, ya kuma yi wannan yunkuri ne har sau uku a jere, duk da cewa bai nasara ba; sakamakon harbe wasu sojoji da aka yi a Abeokuta.
Kazalika, Shugaban Kasa Manjo Janar Aguiyi-Ironsi; ya kara masa girma zuwa Laftanal Kanal, duk dai da cewa; shi ma na wucin gadi ne, a watan Afrilun shekara ta 1966.
Kamar yadda tarihi ya nuna, Janar Murtala ya yi matukar taka muhimmiyar rawar gani a yakin basasar da aka yi a shekara ta 1967, yayin da Laftanal Kanal Ojukwu ke neman balle yankin nan Biyafira daga Nijeriya.
Ko shakka babu, a wannan lokaci ne Janar Ramat ya jagoranci rundunar sojin da suka murkushe sojojin Biyafira tare da kawo karshen yakin basasar baki-daya, kamar yadda ya bayar da sanarwa a ranar 21 ga watan Satumbar shekara ta 1967.
Sojojin da suka yi juyin mulki na uku a Nijeriya, su ne suka nada Janar Murtala a matsayin shugaban kasa, lokacin yana matsayin Birgediya, sannan kuma a watan Janairun shekara ta 1976, aka kara masa girma zuwa Janar mai dauke da anini hudu, ma’ana wanda ya kai kololuwa a aiki ko mukamin soja kenan.
A daidai wannan lokaci ne kuma, Murtala ya kirkiro da sabbin jihohi bakwai tare kuma da bayyana bukatar mayar da babban birnin tarayyar Nijeriya zuwa Abuja, inda kuma ya yi alkawarin mika mulki ga fararen hula a shekarar 1979.
A ranar 13 ga watan Fabreru ne kuma, sai wasu sojoji karkashin jagorancin Dimka; suka yi yunkurin kifar da gwamnatin tasa, yunkurin da bai yi nasara ba, sai dai kashe-kashe da aka yi, amma sun samu nasarar bude wa motar janar din wuta ne; bayan sallar Asuba, a kan hanyarsa ta zuwa ofis a cikin garin Legas.
Babu shakka, a wancan lokaci ‘yan Nijeriya da dama sun yi jimamin rashinsa da aka yi tare da yin Allah wadai da kisan gillar da aka yi masa.
Bayan mutuwar tasa ne kuma, sai aka nada mataimakinsa; Laftanar Janar Obasanjo, a matsayin sabon Shugaban Kasar Nijeriya.
Allah ya jikansa da rahma, ya kuma gafarta masa dukkanin kura-kurensa baki-daya, amin.