ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Thursday, July 9, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

RIGATA 2025: Mun Shirya Tsaf Don Baje Kolin Al’adun Gargajiya Kamar Yadda Aka Saba

by Abdullahi Yelwa
1 year ago
Rigata

Alummar Masarautar Yauri da ke a kudancin Jihar Kebbi, sun shirya tsaf, domin gudanar da bikin gargajiya na Rigata.

An shafe sama da shekaru 200 ana gudanar da wannan bikin gargajiyar wanda kuma ba a ciki ganin irinsa, a kasar nan ba, saboda ana gudanar da bikin ne, kan tudu da kuma gudanar da wasanni, a kan Kogin Neja.

  • Sin Ta Samar Da Yuan Biliyan 6.66 Don Gudanar Da Ayyukan Farfado Da Kauyuka Dake Yankunan Kananan Kabilu
  • Kar Ku Tayar Da Hankalinku Kan Cutar Tsuntsaye – Ma’aikatar Lafiya Ta Kano

Kazalika, ana gudanar kade-kade da raye-raye, wasanni a kan kogi da kuma nuna alkarcin fannin aikin noma da Allah ya wadaci Masarautar da su.

ADVERTISEMENT

Bkin na da nasaba da hudda a tsakanin ‘yan Adam da kuma dabbibin ruwa, kamar Dorinar ruwa, Kada wadanda suke ke kai wa bil Adama hari, tare da janyo mutuwar su.

Domin a dakile wannan barazanar hakan ke sanya wa a duk shekara,  jaruman Gungu, suka shiga cikin Kwale-Kwale dauke da makamai sun yi farautar irin wadannan mugayen dabbobin ruwan.

LABARAI MASU NASABA

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

Yadda Rikice-rikice Ke Ƙara Ta’azzara Talauci A Arewacin Nijeriya —Rahoto

Suna kuma yin hakan ne, domin su samar da tsaro a kan Kogunna da tabbatar da zirga-zirga a cikin sauki da kuma kara habaka sauran hada-hadar kawuanci a Kogunan.

Bayan zuwa Turwan mallaka a karni na 19, an haramta farautar Dorinar ruwa, sai dai, daga baya, an ci gaba da yi a  bikin na Rigata, domin a nuna irin karfin da Masarautar take da shi, musamman a lokutan bukukuwan aure.

Kai ziyarar da marigayi Sardaunan Sokoto kuma Firimiyan Arewa Sir Ahmadu Bello, a yankin na Yauri, hakan ya sake farfado da bikin na Rigata, wanda lokacin ziyararsa, aka gudanar da wasanni da kuma baje kolin amfanin gona, domin a karrama shi.

Bisa jajircwar Mai Martaba Sarkin Yauri Dakta Mohammad Zayyanu Abdullahi, CON, da kuma namjin kokarin gwamnan jihar, an sake farfado da bikin karo na 42.

Mayar da hankali da Dakta Nasir Idris da kuma, Kauran Gwandu, Gamjin Yauri, ya taimaka matuka wajen farfado da martabar bikin.

Kazalila, tsarin da Gwamna Idris ya samar na daga darajar yawon bude Ido a jihar, hakan ya kara janyo ra’ayin bunkasar bukukuwan gargajiya a jihar.

Misali, manya bukukuwan gargajiya kamarsu, bikin kamun Kifi na kasa da kasa na Argungu da ake gudanarwa a garin Argungu,bikin gargajiya na the Uhola.

Bikin gargajiya na Zuru da ake yi a yankin Geandu, ya taimaka wajen daga darajar yawon bude Ido na jihar  Kebbi a Idon duniya.

Duba da yadda ake gudanar da manyan bukukuwan gargajiya a kasar, sai dai, akwai wasu manyan kalubale nan a ci gaba da gudanar da bukuwan da kuma karancin kudi, musamman domin a ci gaba da gudanar da bukukuwan.

Bukukuwa da dama, sun bace bat, saboda rashin kudin ci gaba da gudanar da su, wasu ma, tun daga matakin farkon fara gudanar da su.

Idan har ana son gudanar da bukukuwan gargajiya su ci gaba da dorewa, dole ne, alumma su bayar da na su goyon bayan, musamman wajen samar da kudade.

Bikin na  Rigata, na daga cikin manyan bukuwan da ke a kasar ana kuma gudanar da bikin ne, a duk shekara a cikin watan Fabirairun.

Ana fara gudanar da bikin ne, ta hanyar baje kolin amfanin gona, sai kuma nuna al’adun gargajiya da kade-kade da kuma raye-raye, tare da yin gasar kokawar gargajiya.

A bikin ana gudanar da gasar wasa da Kwale-Kwale a kan Kogi, inda kuma a bikin ya hada da, ‘yan tawagar kai Amarya tare da yi mata rakiya da kade-kade a  cikin Jirgin Kwale-Kwalen da aka yi masa ado

A baya, ana yi wa Amaryar rakia ne, zuwa gidan mijinsu a cikin Kwale-Kwale, musamman a yankunan da ake da Rafuka.

A 2023, an karamma Gwamnan jihar Dakta Nasir Idris a wajen bikin na bara da wakar Gambara, wacce ita ce ta farko, da aka fara gabatarwa a lokacin bikin.

A yayin da ake shirye-shiryen gudanar da bkin na bana, ‘yan Nijeriya na ci gaba da sa ido, domin su ga yadda bikin na zai gabatar da wasu sabbin dabaru, musamman a bangaren kade-kade.

Rigata
Abdullahi Yelwa
+ postsBio
    This author does not have any more posts.

MASU ALAKA

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji
Rahotonni

Matsalar Tsaro: Masana Sun Firgita Da Fitowar Sabon Bidiyon Bello Turji

June 26, 2026
An Kashe Mutane Da Dama Da Kone Gidajensu A Wani Hari Da Aka Kai Benuwai
Rahotonni

Yadda Rikice-rikice Ke Ƙara Ta’azzara Talauci A Arewacin Nijeriya —Rahoto

June 26, 2026
Noma
Rahotonni

Ƙa’idojin Gudanar Da Biyan Kuɗi Nan Take Domin Kare Kai Daga Zamba

June 26, 2026
Next Post
Ƴansanda Sun Gano Motoci 2 Da Aka Sace A Kano

Ƴansanda Sun Gano Motoci 2 Da Aka Sace A Kano

LABARAI MASU NASABA

Ta’addanci

Sojoji Sun Kashe ’Yan Ta’adda Takwas A Katsina

July 9, 2026
Me Ya Sa Aka Ce Kasar Sin Ta Ceci Tattalin Arzikin Duniya?

Me Ya Sa Aka Ce Kasar Sin Ta Ceci Tattalin Arzikin Duniya?

July 9, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa ONSA Kan Shirin Horon Masu Tsaron Daji ‘Forest Guards’

July 9, 2026
Auto Draft

TCN Ta Kammala Gyaran Layin Wutar Lantarkin Zaria–Funtua 132kV

July 9, 2026
Auto Draft

DSS Ta Kama ‘Yar Jarida Zainab Sodiq Kan Zargin Mallakar Drone Ba Tare da Cikakkun Takardu ba

July 9, 2026
Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa NSA Kan Shirin Samar Da Dakarun Tsaron Daji

Gwamnatin Kaduna Ta Yaba Wa NSA Kan Shirin Samar Da Dakarun Tsaron Daji

July 9, 2026
Shaidar EFCC Ya Ce Sirika Bai Sanya Hannu A Takardun Kwangilar Naira Biliyan 2 Ba

Shaidar EFCC Ya Ce Sirika Bai Sanya Hannu A Takardun Kwangilar Naira Biliyan 2 Ba

July 9, 2026
’Yan Bindiga Sun Kashe Farfesa Har Lahira A  Jihar Benuwai

’Yan Bindiga Sun Kashe Farfesa Har Lahira A Jihar Benuwai

July 9, 2026
Sojoji Sun Kashe ‘Yan Bindiga, Sun Ceto Mutane A Kaduna Da Filato

Sojoji Sun Hallaka Shugaban ’Yan Bindiga, Sun Daƙile Hare-hare A Zamfara

July 9, 2026
Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Iran Da Su Aiwatar Da Cikakkiyar Takardar Bayanin Fahimtar Juna Da Aka Cimma

Sin Ta Yi Kira Ga Amurka Da Iran Da Su Aiwatar Da Cikakkiyar Takardar Bayanin Fahimtar Juna Da Aka Cimma

July 8, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.