Bayanai daga kamfanin harkokin layin dogo na kasar Sin sun bayyana cewa, a cikin watanni 7 na farkon shekarar 2023, jarin da kasar Sin ta zuba a fannin gina layin dogo ya kai Yuan biliyan 371.3 kwatankwacin dalar Amurka biliyan 51.9, wanda ya nuna karuwar kashi 7 cikin dari idan aka kwatanta da na shekarar da ta gabata.Â
Kamfanin ya bayyana cewa, a cikin watan da ya gabata, kammala ayyukan gyare-gyaren da aka yi a wasu layukan dogo, ya kawo saukin tafiye-tafiyen fasinjoji, da kuma kara karfin sufuri da inganci, musamman a yankin yammacin kasar.
Alal misali, aikin inganta sashen Xining-Golmud na layin dogon Qinghai-Tibet ya ba da damar zirga-zirgar jiragen kasa masu saurin tafiya na kilomita 160 cikin sa’a guda, wanda hakan ya saukaka jigilar fasinjoji zuwa Golmud da Delingha, wuraren da ake samun yawan tafiye-tafiye a lardin Qinghai da ke arewa maso yammacin kasar Sin.
A watan Yuli, An samu fasinjoji miliyan 406 wadanda suka yi tafiye-tafiye da jiragen kasa na kasar. A cikin watan, jiragen kasa 10,169 suka yi aiki a kullum, adadin da ya karu da kashi 14.2 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin wannan lokaci a shekarar 2019, a cewar kamfanin. (Yahaya)