Ma’aikatar kula da cinikayya ta kasar Sin, ta bayyana a yau cewa, jarin kai tsaye na ketare da aka zuba a babban yankin kasar, wanda kuma ake juyawa, ya fadada da kaso 15.6 a kan na bara, inda ya kai yuan triliyan 1.00376, a watanni 9 na farkon bana.
Alkaluma daga ma’aikatar sun nuna cewa, idan aka kwatanta da takardar kudin dalar Amurka, jarin ya karu da kaso 18.9, zuwa dala biliyan 155.3.
Bangaren bayar da hidima, ya samu karuwar jarin da kaso 6.7 a kan na bara, zuwa yuan biliyan 741.43, yayin da na masana’antar fasahohin zamani ya karu da kaso 32.3 a kan na bara.
Jarin a bangaren kera kaya bisa fasahohin zamani ya karu zuwa kaso 48.6 daga adadin da ya kasance a makamancin lokacin a bara, yayin da na bayar da hidima a masana’antar ta fasahohin zamani ya karu zuwa kaso 27.9 a kan na bara.
Yayin wani taron manema labarai a yau, kakakin hukumar raya cinikayya da kasa da kasa ta kasar Sin, Sun Xiao, ya bayyana cewa, kamfanonin kasashen waje dake kasar Sin, na cike da kwarin gwiwa kan kasuwar kasar, haka kuma suna jinjinawa muhallin kasuwanci na kasar Sin da ma manufofin raya tattalin arzikin kasar. (Fa’iza)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp