Alkaluman kididdigar da ma’aikatar kasuwancin kasar Sin ta bayar a yau Laraba, ta ce, a shekarar 2022, yawan jarin waje da kasar Sin ta yi amfani da su a zahiri, ya kai yuan triliyan 1.23268, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 189.13, adadin da ya karu da kashi 8% kan makamancin lokaci na shekarar 2021. Hakan dai yana tabbatar da cewa, kudaden waje da kasar Sin ta yi amfani da su a zahiri ya karu yadda ya kamata.
Kaza lika zuba jari daga muhimman wuraren duniya ya karu gaba daya. Wuraren dake da saurin karuwar zuba jari a Sin sun hada da Koriya ta Kudu, da Jamus, da Ingila da sauransu, wadanda suka karu da kashi 64.2%, da kashi 52.9%, da kuma kashi 40.7%, bisa makamancin lokaci na 2021. Jarin da tarayyar Turai, da kasashen da suka shiga shawarar “Ziri daya da hanya daya”, da kuma kasashe mambobin kunigyar ASEAN kudu suka zuba a Sin, su ma sun karu da kashi 92.2%, da 17.2% da kuma 8.2%. (Safiyah Ma)