Ma’aikatar cinikayya ta kasar Sin, ta ce jarin waje na kai tsaye dake shigowa Sin wato FDI, ya kai yuan tiriliyan 1.04 cikin watanni 11 na farkon shekarar bana.
Alkaluman ma’aikatar ya nuna cewa, jarin na FDI da ake amfani da shi a babban yankin kasar ya kai yuan tiriliyan 1.04, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 146.45 cikin watannin 11, wanda ya yi kasa da na shekarar da ta gabata da kaso 10 bisa dari.
- Sin Ta Tsara Kyawawan Sharuddan Janyo Jarin Waje
- Sin Ta Bayyana Matukar Adawa Ga Amurka Game Da Batun Sayarwa Taiwan Makamai
Tsakanin watannin 11, sabbin kamfanoni masu zuba jarin kai tsaye 48,078 ne suka bude hada hada a kasar ta Sin, adadin da ya karu da kaso 36.2 bisa dari a shekara.
Har ila yau, a cewar ma’aikatar, alkaluman FDI a fannin kamfanonin manyan fasahohi ya daga da kaso 1.8 bisa dari a shekara, yayin da na fannin samar da kayayyakin bukata a fannin kiwon lafiya ya daga da kaso 27.6 bisa dari, sai kuma na fannin sadarwa da ya karu da kaso 5.5 bisa dari.
Kaza lika, a tsakanin wannan wa’adi, FDI daga kasashen Birtaniya ya kasu da kaso 93.9, daga Faransa ya karu da kaso 93.2, sai na Netherlands da ya karu da kaso 34.1 bisa dari.
Game da halin tattalin arziki da kasar Sin ke ciki, mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya bayyana yayin taron manema labarai na Alhamis din nan cewa, ci gaban kasar Sin na fuskantar karin yanayi mai inganci, sama da nau’o’in kalubalen da yake fuskanta, kuma muhimman matakan da kasar ke aiwatarwa, na farfadowa da inganta tattalin arziki a tsawon lokaci ba su sauya ba, kana dukkanin ginshikai dake goya baya ga samar da ci gaba mai inganci, na haifar da karin kyautatuwar yanayi a fannin.
Kafin hakan, yayin wata ganawa da manema labarai, wakilin asusun ba da lamuni na duniya IMF Steven Alan Barnett, ya ce a shekarar bana, Sin za ta samar da gudummawar kaso 1 bisa 3 na karfin bunkasar tattalin arzikin duniya. Barnett ya yi hasashen cewa, tattalin arzikin Sin zai ci gaba da bunkasa a shekarar 2024.
Game da hakan, Wang Wenbin ya ce cibiyoyin kasa da kasa masu yawa, ciki har da IMF, da hukumar bunkasa hadin gwiwar raya tattalin arziki da samar da ci gaba, a baya bayan nan sun daga mizanin hasashen su na ci gaban tattalin arzikin Sin, a shekarar nan ta bana, da ma shekarar dake tafe. Hakan a cewarsa na nuna cewa, Sin ta zama babban jigo dake ingiza ci gaban tattalin arzikin duniya. (Mai fassara: Saminu Alhassan)