Jarumar masana’antar shirya fina-finai ta kudancin Nijeriya, Nollywood, Mercy Aigbe ta wallafa hotunanta da kanta da ke nuna ta na gudanar da Ibadar aikin Hajji a kasa mai tsarki ta Saudiyya.Â
Jarumar wacce cikin godiyar Allah take nuna alfarinta da kasancewa cikin musulunci tare da addu’ar Allah ya karbi ibadun bayinsa.
Idan za a tuna dai Mercy Aigne ta Musulunta ne bayan da ta auri wani mai yin film, Kazeem Adeoti a shekarar 2022.
A cikin hotunan da ta wallafa a shafinta na Instagram, ta na tare da mijinta, Adeoti.
Ta rubuta da cewa, “Muna addu’ar Allah ya amshi ibadunmu a wannan rana ta musamman ta Ibada, amin.”
Ga wasu hotunan kamar yadda ta wallafa a shafinta: