Yau Asabar 24 ga wata, shugaban kasar Amurka Joe Biden ya rattaba hannu kan dokar ba da izinin tsaron kasa ta shekarar kasafin kudi ta 2023, wacce ta kunshi ayoyi marasa kyau masu yawa da suka shafi kasar Sin.
Game da wannan batu, kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin ya bayyana cewa, kasar Sin ta yi suka da kakkausar murya, kan matakin Amurka na rattaba hannu kan “Dokar ba da izinin tsaron kasa ta shekarar kasafin kudi ta 2023”, wadda ke kunshe da munanan abubuwan da suka shafi kasar Sin, kuma bangaren Sin din ya gabatar da korafi mai karfi ga bangaren Amurka.
Kakakin ya jaddada cewa, kasar Sin ta bukaci Amurka da ta aiwatar da muhimmiyar matsayar da shugabannin kasashen biyu suka cimma a yayin ganawarsu a taron kolin G20 da aka yi a tsibirin Bali, tare da yin watsi da ra’ayin yakin cacar baka, a maimakon haka ta rungumi gaskiya da adalci, kan ci gaban kasar Sin, da huldar dake tsakanin kasashen biyu, ta kuma kaucewa aiwatar da wasu munanan ayoyi masu alaka da kasar Sin dake cikin dokar.
Kakakin ya kara da cewa, kasar Sin za ta dauki kwararan matakai masu karfi, don kare muradunta na mulkin kai, da na tsaro da samar da ci gaba. (Mai fassara: Bilkisu Xin)