Shugaban babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong ya gabatar da jawabin murnar shiga sabuwar shekara ta kafofin CGTN da CRI da kuma yanar gizo a yau Lahadi, 1 ga watan Janairun shekarar 2023, inda ya taya masu kallo da sauraro na ketare murnar sabuwar shekara. Ga jawabinsa:
Aminai masu kallonmu da masu sauraronmu:
A yayin da muka shiga shekarar 2023 mai cike da fatan alheri cikin hasken rana mai dumi na yanayin sanyi, ina muku gaisuwa daga nan birnin Beijing.
A cikin shekarar 2022 da ta kare ba da dadewa ba, an gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20 cikin nasara, inda aka tabbatar da burin ingiza aikin farfadowar al’ummar Sinawa daga dukkan fannoni ta hanyar zamanintarwa irin na kasar Sin. A matsayinsa na mai tafiya da sabon zamani, da nuna gaskiya da nuna sakamakon da kasar Sin ta samu a sabon zamani, CMG ya gabatar da shirye-shiryen dake shafar wannan gaggarumin taron ga masu kallonmu dake fadin duniya, kuma ya tsara shirye-shirye da dama kamar “Jagora” da “Sakamakon da kasar Sin ta samu a cikin shekaru goma da suka gabata”, domin bayyana babban sakamakon da kasar Sin ta samu a cikin shekaru goma da suka wuce, duk wadannan shirye-shirye sun samu yabo matuka daga masu kallonmu na cikin gida da na ketare.
A cikin shekarar da ta gabata, mun yi kokarin yin kirkire-kirkiren da suke hada tunani da fasaha, domin cimma burin samar da shirye-shirye masu inganci ga masu kallonmu. Yayin da CMG yake gabatar da rahotanni kan gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na birnin Beijing, ya hada ruhin wasannin Olympics da al’adun gargajiyar al’ummar Sinawa waje daya, kuma ya nuna wasannin karkara da karkara mai laushi ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani, inda shugaban hukumar shirya gasar wasannin Olympics ta kasa da kasa Thomas Bach ya yaba da cewa, aikin gabatar da rahotanni game da gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing na CMG, ya kai matsayin koli a tarihi. Kana shirye-shirye masu inganci dake shafar al’adun gargajiyar kasar Sin da suka hada “Kasar Sin da aka nuna da litattafan tarihi” da “Kasar Sin da aka nuna da zane-zane da rubutattun wakoki” da sauransu, cikakken bayani ne da aka yi kan dalilin gadar wayewar kai ta al’ummar Sinawa, shi ma kokarin da ake yi domin cimma zaman jituwa tsakanin mabambantan wayewar kan bil Adama. Haka zalika shiri kan murnar bikin bazara da bikin murnar tsakiyar kaka, da bikin murnar shiga sabuwar shekara da CMG ya shirya, sun jawo hankalin masu sha’awar al’adun kasar Sin dake ketare matuka. Ban da haka, bikin nuna fina-finan kasar Sin, da bikin nuna fina-finan kasar Sin a nahiyar Latin Amurka, da bikin nuna fina-finan kasar Sin a nahiyar Afirka da aka shirya, sun kasance tamkar wata gadar sada zumunta da mabambantan wayewar kai dake tsakanin al’ummomin kasashen duniya baki daya ta hanyar fina-finai.
A shekarar bara, mun shirya dandalin taruka da ayyuka iri daban daban na kafofin watsa labarai masu yawan gaske, alal misali dandalin taron kirkire-kirkiren kafofin watsa labarai na kasa da kasa karo na farko, da babban dandalin taron cudanya kan al’adu tsakanin kasar Sin da kasar Argentina, da dandalin taro kan hadin gwiwar kafofin watsa labarai na kasar Sin da kasashen Larabawa da sauransu. Makasudin shi ne kara karfafa tsarin hadin gwiwa tsakanin kafofin watsa labarai na shiyya shiyya, ta yadda za a kara zurfafa zumuncin da cudanya dake tsakanin takwarorin kafofin watsa labaran kasa da kasa. Bayan babban taron wakilan JKS karo na 20, mun shirya aikin cudanyar kafofin watsa labarai na kasa da kasa mai taken “Kasar Sin da duniya a sabon zamani” a jere har sau 58, inda muka yi cudanya da abokanmu na kasashen duniya kan ma’anar zamanintarwa irin na kasar Sin, da rawar da take takawa ga ci gaban duniya, ayyukan da suka samu amincewa daga kafofin watsa labaran kasa da kasa sama da 2000.
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sha jaddada cewa, kasar Sin tana tsayawa kan manufar goyon bayan adalci da ci gaban wayewar kan bil Adama, tana kuma kokarin samar da hikima da dabarunta domin tabbatar da zaman lafiya da ci gaba a fadin duniya. Karfin yada manufa wata muhimmiyar alama ce ta kafar watsa labarai ta kasa da kasa, gabatar da labari na gaskiya, abu ne mai muhimmanci ga kafar watsa labarai, don haka mun kyautata tsarin farautar labaran da suka shafi kasashen duniya a shekarar da ta gabata, domin gabatar da labaran da suka fi jawo hankalin al’ummar kasashen duniya a kan lokaci, kana mun kara harsunan da muke watsa shirye-shirye daga 44 zuwa 68, wadanda suke gabatar da labarai ga kasashe da shiyyoyi 233 dake fadin duniya. Manufarmu ita ce yada matsayi da dabarar kasar Sin mai adalci ga zamantakewar al’umma, musamman ma kan rikicin dake tsakanin kasar Rasha da kasar Ukraine, da kokarin da ake yi domin kandagarkin yaduwar annobar cutar COVID-19 da sauransu.
A cikin sabuwar shekara ta 2023, za mu ci gaba da nuna himma da kwazo domin nuna wa al’ummar kasashen duniya sabon ci gaban da kasar Sin ta samu a sabon zamanin da ake ciki. Bana shekaru 10 ke nan da aka gabatar da shawarar ziri daya da hanya daya, don haka, za mu ci gaba da yin cudanya da sauran kafofin watsa labaran kasa da kasa domin ingiza mu’amalar mabambantan wayewar kan bil Adama, tare da gina kyakkyawar makomar bil Adama ta bai daya yadda ya kamata.
Sinawa su kan bayyana cewa, “Duwatsu da koguna suna kara kyan gani a yanayin bazara, kamshin furanni da ciyayi ya karade ko’ina sakamakon kadawar iskar bazara.” Yanzu bazara tana nan tafe, ina son yin amfani da wannan dama wajen sake taya ku murnar sabuwar shekara, ina fatan za ku kasance cikin koshin lafiya. Na gode. (Mai fassarawa: Jamila daga CMG Hausa)