A ‘yan kwanakin nan, rukunin gidajen rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) ya kaddamar da jerin tattaunawa da manyan jami’ai da kuma zantawa mai taken “Shawarwarin kasar Sin da makomar duniya”, inda aka gayyaci manyan jami’ai daga MDD, da shugabannin kungiyoyin kasa da kasa, da baki daga bangarorin siyasa, kasuwanci, ilimi da kafofin watsa labarai na kasashen Amurka, Faransa, Aljeriya, Masar da sauran kasashe.
Baki daga dukkan kasashen sun amince gaba daya cewa shawarar inganta jagorancin duniya (GGI) ta zo a kan gaba. Shawarar ta kasar Sin ta nuna yadda babbar kasa take sauke nauyin da ke wuyanta ga duniya.
A wata hira ta musamman da ya yi da CMG, Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya bayyana cewa, jerin shawarwarin da shugaban kasar Sin ya gabatar sun samar da mafita a kan ainihin batutuwan da suka shafi duniya baki daya, kuma suka yi matukar dacewa da al’amuran da ke ci wa MDD tuwo a kwarya, kana suka nuna kyakkyawan hangen nesa da kuma sauke nauyin da ke wuyan babbar kasa.
Kazalika, a cikin wata hirar ta musamman da CMG, babbar darektar hukumar cinikayya ta duniya (WTO) Ngozi Okonjo-Iweala, ta yi kyakkyawan nazari kan shawarar inganta jagorancin duniya, ta kuma yaba da kokarin da kasar Sin ke yi wajen kiyaye tsarin cinikayya a duniya wanda ya fi maida hankali a kan turbar WTO, kana ta yaba da gudummawar da kasar Sin ke bayarwa wajen tallafa wa ci gaban kasashe masu tasowa. (Abdulrazaq Yahuza Jere)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp