Robert Lewandowski ya bi sahun Lionel Messi da Cristiano Ronaldo a matsayin mutum na uku a tarihi da ya zura kwallaye 100 a gasar Zakarun Turai ta UEFA Champions League da kwallon da ya ci ta baya-bayan nan a wasan da suka buga da kungiyar kwallon kafa ta Brest a ranar Talata a gasar Zakarun Turai, yayin da suke kan gaba wajen neman tikitin zuwa zagaye na 16 na gasar.
Kwallon farko da Lewandowski ya ci ita ce ta 100 da ya ci a gasar kuma ita ce ta sa ya shiga cikin jerin ‘yan wasan da suka cimma wannan mataki na ‘yan wasan da suka zura kwallaye 100 a tarihin gasar. Lewondowski mai shekaru 36 ya zura kwallonsa ta 100 a minti na 10 sai kuma ta 101 a minti na 93 a wasan da Barca ta doke Brest a filin wasa na Olympico Luis Companys.
- Lookman Na Shirin Lashe Kyautar Gwarzon Dan Wasan Afirka Na 2024
- Karancin Takardar Kudi: Masu POS Da Bankuna Na Wasa Da Hankulan Jama’a
Kafin yanzu Cristiano Ronaldo da Lionel Messi ne kadai ‘yan wasan da suka jefa kwallaye fiye da 100 a gasar Zakarun Turai, inda Ronaldo ke da kwallaye 140 a wasanni 183 da ya buga a manyan kungiyoyin kwallon kafa da suka hada da Manchester United, Real Madrid da Jubentus, sai Messi da ya jefa 129 a wasanni 163 da ya buga a gasar sai kuma yanzu Lewondowski da ke da kwallaye 101 a raga a wasanni 125.
Lewondowski ya jefa wa Borrusia Dortmund kwallaye 17, Bayern Munich 69 yayin da ya jefa wa Barcelona kwallaye 15 a gasar Zakarun Turai. Tsohon dan wasan Lyon da Madrid Karim Benzema ne ya fi kusa da kamo wannan mataki yayin da ya jefa kwallaye 90 a wasanni 152 a gasar Zakarun Turai, amma yanzu ya na kungiyar Al Ittihad ta Saudi Pro League.