Gwamnatin jihar Jigawa ta kaddamar da rabon kayan noma na Naira biliyan 1.5 don shirin ba da lamuni na noma kashi na biyu na ma’aikatan gwamnati na 2025.
An fara shirin ne a shekarar 2024 inda jihar ta amince da Naira biliyan 3, wanda ma’aikatan gwamnati da sauran jama’a 8,828 suka amfana da shirin.
- Remi Tinubu Ta Bada Gudunmawar Naira Biliyan 1 Ga Wadanda Ambaliyar Ruwan Neja Ta Shafa
- Ƴansanda Sun Kama Ƴan Uwa da Wasu Biyu Kan Ƙirkirar Garkuwa Da Kansu A Abuja
Da yake jawabi a wajen bikin kaddamar da rabon kayan a Dutse, babban birnin jihar, Gwamna Umar Namadi, wanda mataimakinsa, Engr. Aminu Usman ya wakilta, ya ce shirin ya yi daidai da manufofin gwamnatinsa na inganta jin dadin ma’aikatan gwamnati ba sai ta hanyar albashi kadai ba.
Ya bayyana cewa, an tsara bayar da lamunin noma ne domin taimakawa ma’aikata wajen kara samar musu da hanyoyin samun kudin shiga tare da bayar da gudummawar samar da abinci ga kasa.
Engr. Aminu ya kara da cewa, gwamnatin jihar ta gamsu da sakamakon kashi na farko da aka gabatar, inda ya ce hakan ya kara karfafa gwiwar zuba jari a shirin.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp