Gwamnatin jihar Jigawa, ta jaddada aniyarta na ci gaba da rike matsayinta na jihar da ta zamo Zakara a tsakanin jihohin kasar nan wadda al’ummarta ba sa yin bahaya a bainar jama’a.
Kwamishinan yada labarai, wasanni da al’adu, Sagir Musa Ahmed da Kwamishinan kula da albarkatun ruwa Ibrahim Muhammed Garba da kwamishinan kula da Muhalli Dakta Nura Ibrahim Kazaure na jihar ne suka bayar da wannan tabbacin.
- Hanyoyin Da Iyaye Ke Taimaka Wa ‘Ya’yansu Samun Nasarar Karatu (1)
- Hukumar Jin Daɗin Alhazai Ta Yi Wa Maniyyata 3,918 Rijista A Cikin Kujeru 5,001 A Sakoto
Sun sanar da hakan ne a taron manema labarai na hadaka a Kaduna, bayan da kwamitin jihar da gwamnatin jihar ta kafa don ci gaba da sa ido kan rike wannan matsayin da sauran masu ruwa da tsaki na jihar sun gudanar da taro a Kaduna.
Kwamishinan yada labarai, a na sa vangaren ya ce, sun zo Kaduna ne don tattauna wa kan yadda Jigawa za ta ci gaba da rike wannan matsayin na ta da Gwamnatin Tarayya ta ayyana jihar a 2022 a matsayin jihar da alummarta ba sa yin bahaya a bainar jama’a.
Ya ce, hatta a 2023, an karrama Jigawa da lambar yabo a matsayin jihar da al’aumar ta, ba sa yin bahaya a bainar jama’a.
Sagir ya ce, taron zai fitar da wani tsari wanda gwamnatin jihar za a wanzar da shi don ya bata damar ci gaba da rike wannan matsayin na ta.
Shi ma Kwamishinan kula da albarkatun ruwa ya ce, wannan damar ta haifar da ana gudanar da aikin tsaftace gari da ake gudanar wa a duk wata a jihar .
Shi kuwa na kula da muhalli ya ce, gwamnatin jihar a karkashin mulkin gwamnan jihar Mal. Umar NamadI, ta dauki matakan da suka dace don a tabbatar da cew jihar ta ci gaba da rike wannan matsayin na ta.