Matatar mai ta Dangote ta ce za ta fara jigilar mai zuwa gidajen mai a faɗin Nijeriya, amma hakan ya jawo saɓani tsakakinta da ƙungiyar NUPENG.
NUPENG na ganin motocin Dangote na barazana ga sana’arsu, tana kuma son direbobin Dangote su zama mambobinta tare bin dokokinta.
- Fadar Shugaban Ƙasa Ta Mayar Wa Atiku Martani Kan Cewar ‘Yan Nijeriya Na Fama Da Yunwa
- Tawagogin Sin Da Na Amurka Sun Sake Tattaunawa Game Da Batutuwan Tattalin Arziki Da Cinikayya A Rana Ta Biyu
Ƙungiyar ta kuma nemi motocin Dangote su riƙa bin layi kamar sauran masu dako ke yi, ba a nuna musu fifiko ba.
Sai dai Dangote ya ce kamfaninsa mai zaman kansa ne, kuma yana da ’yancin cin gashin kansa.
Matatar na son ta sayar da mai kai tsaye ga gidajen mai ba tare da ‘yan tsakiya ba, don rage tsadarss.
Duk da cewar an yi yarjejeniya tsakanin ɓangarorin biyu, rikici ya sake ɓarkewa bayan NUPENG ta ce Dangote bai cika alƙawari ba.
Amma matatar ta musanta zargin, inda ta bayyana cewa ma’aikatanta na da damar shiga ƙungiya idan sun so, amma ba dole ba ne.