Gwamnatin Jihar Kaduna da gwamnatin kasar Jamus za su kula alaka mai karfi ta fuskar tattalin arziki don samar da ci gaba mai dorewa a jihar.
In ba a manta ba, a watan Disambar 2023, Gwamna Uba Sani ya ziyarci Hukumar Haɗin kai ta Jamus (GIZ) a kokarin Gwamnan na janyo masu zuba jari a jihar Kaduna don ganin jihar a karkashin gwamnatinsa ta samu daukaka da habbaka mai dorewa.
- Juyin Mulki: Rufe Iyakar Nijeriya Da Nijar Ya Jefa Arewa Cikin Tsaka Mai Wuya – Aliero
- Gwamnatin Kaduna Za Ta Sa Kafar Wando Da Masu Hakar Ma’adanai Ba Bisa Ka’ida Ba
Sakamakon wannan ziyara, GIZ ta bayyana shirinta na marawa jihar baya domin cimma burinta na ci gaba.
A ranar 16 ga watan Janairu, wakilai daga GIZ, karkashin jagorancin Daraktanta, Dr. Markus Wagner, ta kawo wa gwamnatin jihar Kaduna ziyarar kwanaki biyu. Makasudin ziyarar dai ita ce tattaunawa da karfafa dangantakar tattalin arziki tsakanin bangarorin biyu.
Tawagar GIZ ta samu kyakkyawar tarba daga Gwamna Uba Sani da wasu manyan jami’an gwamnati, inda daga baya aka gudanar da liyafar cin abinci don kara karfafa dangantakar da ke tsakanin bangarorin biyu.
A yayin tattaunawar wadda aka ci gaba a washegari, mataimakiyar gwamna Dr. Hadiza Sabuwa Balarabe ta jagoranci manyan jami’an gwamnati wajen tattaunawa kan wasu bangarori da jihar ke bukatar tallafi daga gwamnatin Jamus. Waɗannan muhimman bangarori sun haɗa da fannin makamashi, samar da sauyi a fannin zamani (dijital), haɓaka saka hannun jari, da noma.
Dr. Wagner ya nuna jin dadinsa da irin karramawar da aka yi masa, ya kuma kara jaddada aniyar GIZ na tallafawa jihar Kaduna wajen samun ci gaba mai dorewa da samar da ayyukan yi.
Mataimakiyar Gwamnan, a madadin gwamnatin jihar, ta godewa GIZ bisa hadin gwiwar da suka yi, tare da ba su tabbacin jajircewar jihar wajen yin amfani da wannan hadin gwiwa.