Tun farkon bana, jihar Xinjiang ta kasar Sin, ta kara karfin ba da shawara kan yadda za a samarwa daliban da suka kammala karatun jami’o’i aiki, da ma fito da manufofin ba da jagoranci, don taimakawa wadannan dalibai samun aiki yi ta hanyoyi daban-daban.
Kwanan baya, an kaddamar da wani taron daukar ma’aikata na shekarar 2023 a gundumar Wushi, inda aka samar da guraben aikin yi fiye da 600 dake shafar bangarorin albarkatun kwadago da ba da hidimar yawon shakatawa da aiwatar da harkokin cinikin yanar gizo da sauran sana’o’i 35.
Daga watan Janairu zuwa Yuni na wannan shekara, an gudanar da bikin baje kolin guraben ayyukan yi na musamman ga daliban da suka kammala kwalejoji sama da 1,300 a sassa daban-daban na jihar Xinjiang, ta hanyar shirya rangadin daukar ma’aikata na hadin gwiwa a manya da matsakaitan birane a jihar, da ba da jagoranci ga kamfanoni da su gudanar da tarukan daukar ma’aikata a jihar, da sauran hanyoyin taimakawa dalibai samun aikin yi, don ingiza aikin daukar ma’aikata daga makarantu gaba. (Amina Xu)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp