A makon jiya, aka cika kimanin shekaru 32 da kafuwar Jihar Yobe; Jihar da aka kirkiro a ranar 27 ga watan Agustan 1991, a lokacin shugaban mulkin soja, Janar Ibrahim Babangida. Bisa wannan dogon lokaci da Jihar ta dauka, jama’a da dama za su so sanin ina aka taso, ina ake kuma ina za a je a karin wasu shekarun masu zuwa ta fuskar bunkasar ci gaban al’amurran yau da kullum na rayuwar al’ummar Jihar baki daya. Saboda ko ba komai, daya daga cikin dalilin kirkiro jiha ko karamar hukuma shi ne domin kusanto da ci gaba daf da al’umma; don suma su tabbatar ana damawa da su a fannin ci gaba.
Kowace gwamnati babban abin da ya dace ta fi mayar da hankali a kai shi ne fadi-tashin inganta rayuwar al’ummar da take wakilta. Amma kuma manazarta al’amurran yau da kullum, kowane lokaci suna da abin fada wajen tofa albarkacin bakinsu dangane da muhimman abubuwan da su ake amfani da su wajen auna ci gaban kowane yanki, jiha ko tarayya baki daya. Bugu da kari kuma, muhimman bangarorin da masana suka fi bai wa muhimmanci wajen auna kimar ci gaban kowace jihar su ne; samun kyakkyawan shugabanci wanda zai bayar sa damar aiwatar da manufofin gwamnati wanda zai kai ga ci gaba, sai fannin Ilimi, kiwon lafiya, aikin gona, Kasuwanci da masana’antu tare da kirkiro sabbin habyoyin samun aiki da bunkasar tattalin arzikin kowace jiha.
- Shugaban Kasar Zambia Zai Kawo Ziyarar Aiki A Kasar Sin
- Hukumomin Sin Sun Fitar Da Wasu Ka’idoji Don Inganta Tsaron Wuraren Hakar Ma’adinai
Sauran sun hada da inganta harkokin tsaron rayuwa da dukiyar al’umma, kokarin gwamnati wajen hada kan al’umma da wayar da kansu dangane da al’amarran yau da kullum na ci gaban zamani. An kirkiro Jihar Yobe daga tsohuwar Jihar Borno da ke Arewa Maso Gabashin Nijeriya, jiha ce wadda kimanin kaso 75 cikin dari na al’ummar ta manoma ne, kana ta kunshi kananan hukumomi 17- Bade, Bursari, Damaturu, Geidam, Gujba, Gulani, Fika, Fune, Jakusko, Karasuwa, Machina, Nangere, Nguru, Potiskum, Tarmuwa, Yunusari da Yusufari.
A bangaren sha’anin gwamnati, Gwamnoni 8 ne suka shugabanci Jihar Yobe; na mulkin soji da na farar hula, kamar haka: Gwamna Sani Daura Ahmad: Mataimakin Sufeto Janar na Yan-sanda (AIG) kuma shi ne farkon gwamnan Jihar Yobe, wanda ya dora harsashen gudanar da Jihar, zuwa mika mulki ga zababben gwamnan farar hula na farko, Bukar Abba Ibrahim a jamhuriya ta uku.
Gwamna Bukar Abba Ibrahim: shi ne Gwamna na biyu kuma zababbe na farko da ya rike ragamar mulkin Jihar Yobe daga 1992 zuwa 1993, kuma ya sake dawowa karagar Gwamnan Jihar daga 29 ga watan Mayu 1999 zuwa 29 Mayu 2007 a karkashin jam’iyyar ANPP.
Gwamna Dabo Aliyu: Mataimakin Sufeto Janar na Yan-sanda (Mai ritaya) ya rike gwamnan Jihar Yobe a karkashin mulkin soja, tsakanin Watan Disamban 1993 zuwa watan Agustan 1993, a lokacin marigayi Janaral Sani Abacha.
Gwamna Group Captain John Ben Kalio ya mulki Jihar Yobe daga watan Agustan 1996 zuwa Augustan 1998, lokacin Janaral Sani Abacha.
Gwamna Colonel (Mai ritaya) Musa Mohammed: ya kasance Gwamna a Jihar Yobe, daga watan Agustan 1998 zuwa Mayu 1999, lokacin Janaral Abdulsalami Abubakar. Inda ya sake mika mulkin Jihar ga zababben Gwamna, Bukar Abba Ibrahim.
Gwamna Sanata Mamman Bello Ali: Wanda ya yi nasarar lashe zaben gwamnan Jihar a 2007 zuwa 2009; lokacin da Allah ya yi masa rasuwa a jinyar da yayi fama da ita a asibitin Florida a kasar Amurika.
Gwamna Ibrahim Gaidam: Sanata Gaidam shi ne Mataimakin Gwamna Mamman Bello Ali, wanda sakamakon mutuwarsa ne aka rantsar da Gaidam don ya gaji maigidansa a shekarar 2009 zuwa 2019- inda ya yi shekara 10 cur a kujerar gwamnan Jihar Yobe.
Gwamna Mai Mala Buni: ya dare a kujerar Gwamnan Jihar Yobe ne bayan da ya lashe zaben da aka gudanar a 2019, inda kuma yanzu haka shi ne Gwamna a wa’adi na biyu; bayan zaben 2023 da ya gabata.
Bugu da kari kuma, a tsarin mulkin Nijeriya, gwamnan jiha shi ne ragamar zartas da al’amurran jiharsa, kuma alhakin ci gaba ko akasin hakan ya na bisa wuyan wadannan gwamnonin da suka mulki Jihar Yobe daga jiya zuwa yau. Wannan ya faru ne bisa cikakken ikon zartaswan da kundin tsarin mulki ya damka a hannun su. Sannan bari ku leka mu gani, shin a cikin shekaru 32 da Jihar ta yi da kirkirowa, wadanne ci gaba aka samu kuma ina aka gaza?
Dakta Usman Muhammad (an canja sunan), malami a Kwalejin ilimi ta Jihar Yobe dake Gashuwa, ya ce duk da manyan kalubalen da Jihar Yobe ta fuskanta na rikicin Boko Haram, wanda ya shafi kowane bangaren rayuwar al’ummar Jihar, matsala ce wadda ta mayar da hannun agogo baya a fannin Ilimi, kiwon lafiya, noma da makamantansu. Amma wani hanzari ba gudu ba, ba zai hana duba kokarin da gwamnatocin baya suka yi ba wanda bai wuce dora tubalin gina sabuwar Jihar, wanda a kansa ne Jihar ta fara takawa da kafafunta.
“Daya daga cikin misalan da za a hanga a matsayin ci gaba, shi ne tsarin mulkin dimokuradiyya, tsarin da zai bai wa dan kasa damar yin zabe. Amma kuma inda gizo ke sakar shi ne; har yanzu a Yobe yanki daya ne yake gudanar da mulkin gwamnatin Jihar, shi ne shiyyar gabashin Yobe (in banda marigayi Sanata Mamman Bello Ali) wanda bayan an zabe shi da shekara 2 Allah yayi masa rasuwa. Amma dukanin sauran gwamnonin daga yankin suka fito, ka ga a dimokuradiyyance ma akwai sauran gyara.” Ya bayyana.
Dr. Usman ya kara da cewa, “Inganta harkokin ilimi shi ne babban ginshikin ci gaba a kowace jiha, kuma a daidai wannan gaba, al’amarin ilimi a Jihar Yobe, har yanzu kawai rubuce yake a kan takardun tsara manufofi, amma ba a aiki ba. Sannan duk da ba za a ce babu ci gaba ba, amma jama’ar Jihar kullum tambaya suke: Ina zancen dokar ta-baci da Gwamna Buni ya sa a fannin Ilimi, tare da makudan biliyoyin naira da aka tara don farfado da ilimin? Saboda a wasu bangarori an samu ci gaba da sabanin hakan a wasu wurare wanda har yanzu ana gidan jiya ne- ana kwan-gaba kwan-baya. Kuma za ka tabbatar da haka ne idan ka kalli yadda yanayin Makarantun mu suke, kanana da manya kusan tsarin a rubuce kawai yake a takardu amma idan an zo wajen aiwatarwa abin babu kyawun gani.”
“Sanin kowa ne cewa tsarin aikin tafiyar da gwamnati ba aikin mutum daya ba ne kuma ba aikin lokaci guda ba ne, tsare-tsare ne da manufofi, gudanarwa da aiwatarwa na dogon zango, matsakaici da gajeren zango. Ya dace jama’ar Jihar su san da wannan, a fanni guda kuma mutanen gwamnati su fahimci haka. Idan an zabe ka gwamna ba ya na nufin za ka kammala kowane aiki a lokacin ka ba, face kawai ka yi kokari wajen ganin cewa ka aiwatar da ingantattun manufofi wadanda za su taimaki Jiharka da al’ummar ka. Amma abin takaici shi ne abin ba haka ba ne, saboda tun bayan kirkiro Jihar Yobe alkawarin daya ne; inganta harkokin ilimi, kiwon lafiya, farfado da walwala da jin dadin jama’a da makamantan su, amma shuru kullum zancen kenan.”
Ya kara da cewa, gini yana dorewa ne idan ya samu ingantaccen harsashi, wanda idan an yi la’akari da halin da sashen ilimi yake a Jihar Yobe, ya nuna cewa gwamnatocin da suka shude ba su tabuka abin a zo a gani ba wajen samar da yanayi mai kyau wanda zai yi tasirin kaiwa gaci a Jihar Yobe.
A hannu guda kuma, shima bangaren kiwon lafiya ba a barshi a baya ba, a matsayin muhimmin al’amarin jin dadin al’umma, bangaren da ya samu sauyi da ci gaba a sassansa da dama tare da tarin kalubale a wasu rukunonin sa a daidai lokacin da Jihar Yobe ke bikin tunawa da cikar Jihar shekara 32 da kafuwa. Yayin da gwamnatoci daban-daban, kama daga gwamnatin Bukar Abba Ibrahim, Marigayi Sen. Mamman B. Ali, Alhaji Ibrahim Geidam, da Gwamna Mai Mala Buni na yanzu, sun yi kokarin inganta harkokin kiwon lafiya, face wani abin damuwa a gwamnatin mai ci shi ne halin da ma’aikatan kiwon lafiya ke ciki wadanda suke fama da karancin samun kulawar da ta dace daga bangaren gwamnati.
Bincike ya tabbatar da cewa, shekarun farko bayan kirkiro Jihar Yobe sun kasance masu inganci a fannin bunkasar tattalin arziki wanda ya hada da samar da kudaden shiga na cikin gida, daukar kwararrun ma’aikata, gina masana’antu domin alkinta albarkatun da Jihar take dasu tare da bunkasa harkokin Kasuwanci; Kamfanin Takin Zamani, Kamfanin Fulawa, Kamfanin Kwanon rufi da Kamfanin fatar buhu da leda, a lokacin gwamnatin Alhaji Bukar Abba Ibrahim. Masana’antun da bayan kammala zangon mulkinsa na biyu suka zama tarihi.
Sakamakon kin farfado da wadannan masana’antu, harkokin Kasuwanci da na tattalin arzikin Jihar sun shiga tangal-tangal, bisa gibin da rashinsu ya haifar a fannin samun kudin shiga, ayyukan yi ga matasa da harkokin Kasuwanci da makamantansu. Watsi da wadannan masana’antu babban kuskure ne kuma hatsari ne ga tsarin tattalin arziki da ci gaban al’ummar Jihar Yobe.
A nashi bangaren, matashin dan siyasa a Kudancin Jihar (Zone B), Kwamaret Abubakar Salisu, ya ce akwai babban tasgaro a sha’anin siyasa da gudanarwa da harkokin gwamnati, rashin daidaiton da ya jawo wasu yankuna suna zargin mayar dasu saniyar ware a harkokin siyasa. Inda ya dace kowace shiyya ta samu wakilci mai ma’ana a sha’anin shugabanci da gudanarwa na gwamnati, saboda a samu hadin kai, fahimtar juna tare da yin aiki wuri guda.
Ya ce, “A Jihar Yobe, kamar sauran al’ummar kasa, mu na kokawa da matsalolin bangaranci da son zuciya, wanda ya yi katutu a zukatan wasu shugabanin gwamnati da siyasar Jiharmu ta Yobe. Wanda y zama wajibi shugabanni su kiyaye tare da dabbaka ka’idojin dimokuradiyya wajen yaki da nuna bangaranci don a samu hadin kai mai dorewa da ci gaba. Dole mu taru mu dakile tsiraru masu hura wutar bambanci da bangaranci ko na kabilanci. Amma a ce mun shekara 32 da kirkirowa amma har yanzu wasu tsiraru ne ke mulkin Jihar ba tare da sakarwa saura mara ba, wannan ya saba wa tsarin dimokuradiyya, ci gaba da wayewa.” In ji shi.
Cikar jihar ta Yobe shekara 32 da kafuwa dai na iya zama wani ma’auni da dukkan masu ruwa da tsaki na jihar za su dora ci gaban jihar da koma-bayan da ta samu a sikeli domin tunkarar shekaru masu zuwa ta fuskantar abubuwan da suka kamata a gyara da kara inganta wadanda aka samu nasara a kansu.