Jihohi 21 da suke fadin Nijeriyar suna neman ciwo rancen kudi da yawansa ya kai naira tiriliyan 1.65 domin cike gibin kasafinsu na 2024 duk da cewa sun samu tulin karin kason kudade daga asusun hadaka na tarayya (FAAC) a shekarar da ta gabata.
Daga watan Yunin 2023 zuwa Yunin 2024, dukkanin jihohin da suke fadin Nijeriya gami da kananan hukumomi 774 sun karbi adadin kudin da ya kai naira tiriliyan 7.6 daga asusun FAAC. Wannan karin sama da kaso 40 cikin 100 da suka samu na kudin shiga, shi ne irinsa na farko mafi yawa kuma an samu nasarar hakan ne sakamakon cire tallafin mai da gwamnatin tarayya ta yi a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
- Darajar Naira: Tsohon Dan Majalisa Da Ya Ci Bashin Karatu N1,200 A Shekaru 47, Yanzu Ya Biya Da Fiye Da Naira Miliyan 3
- Bayan Fafatawa, Ƴan Ƙauye Sun Hallaka Ƴan Bindiga 37 A Zamfara
Binciken da aka gudanar ya nuna cewa an tsara jihohi 36 za su amshi naira tiriliyan 5.54 daga FAAC a wannan shekarar sabanin tiriliyan 3.3 da aka raba musu a shekarar da ta gabata.
A ranar 11 ga watan Yuli ne babban kotun koli ta yanke hukuncin bai wa kananan hukumomi 774 cikakken ‘yancin gashin kansu ta yadda za suke amsar kasonsu daga lalitar gwamnatin tarayya zuwa ga asusunsu kai tsaye, sabanin yadda yake zuwa hannun gwamnonin jihohi da suke yin yadda suka ga dama da kudaden.
A binciken da aka gudanar, ya nuna cewa jihohi 21 da suka nuna aniyarsu na ciyo bashin naira tiliyan 1.650 daga kafofin samun bashi na cikin gida da waje domin cike kowace gibin da ke cikin kasafin 2024. Sauran jihohi 15 kuma zuwa yanzu ba su shigar da tsarinsu na neman ciwo bashin ba.
A cikakken tsarin lafto basukan da aka fitar, Jihar Adamawa ta yunkura domin ciwo bashin naira biliyan 68.46; Anambra naira biliyan 245; Bauchi naira biliyan 59.08; Bayelsa naira biliyan 64; Benuwai naira biliyan 34.69; Borno naira biliyan 41.71; Ebonyi naira biliyan 20.5; Edo naira biliyan 42.71 da kuma Ekiti da za ta ciwo bashin naira biliyan 27.15.
Sauran jihohin sun su ne Jigawa naira biliyan 1.78; Kaduna naira biliyan 150.1; Kebbi naira biliyan 36.7; Katsina naira biliyan 163.87; Kogi naira biliyan 37.08; Kwara naira biliyan 30.76; Osun naira biliyan 12.36; Oyo naira biliyan 133.4; Nasarawa naira biliyan 32.93; Gombe naira biliyan 73.75; Inugu naira biliyan 103, yayin da Imo ta shirya kinkimo bashin naira biliyan 271.34.
Sai dai masana sun fito sun ce akwai bukatar tabbatar da gaskiya da adalci kan makudan kudaden da jihohi suka karba balle a je ga maganar sake ciwo basuka.
Babban daraktan cibiyar wanzar da gaskiya da adalci a tsarin kasafi (CFTPI), Umar Yakubu, ya ce, akwai bukatar jihohi su fito su yi bayanin yadda suka kashe kudaden da suka amsa daga asusun gwamnatin tarayya domin wanzar da gaskiya da adalci.
Ya ce, cire tallafin mai ya janyo gwamnoni sun samu karin kudin shiga mafi tsoka, don haka da bukatar a gano yadda suka tafiyar da karin kudaden da suka samu na jihohi da na kananan hukumomi.
Shi ma wani kwararre, Bictor Agi, ya ce, muddin ba a wanzar da gaskiya wajen tafiyar da kudaden da suke shiga hannun gwamnatoci ba, to tabbas matsalolin da ake fuskanta za ma su ci gaba da karuwa.