Kwanan nan, Jamus ta wallafa wata takarda, a karon farko a tarihinta, mai taken “cikakkiyar dabarun ƙasar Sin,” manufar rage dogaron tattalin arzikinta ga Beijing, tana mai nuna buƙatar gaggawa na “yin taka-tsantsan da haɗarin mu’amala” da ƙasar Sin.Wannan takarda tana yiwa ƙasar Sin laƙabi da “abokiyar harkalla, abokiyar fafatawa, kuma abokiyar adawa a dabarance.”
A cikin saƙonsa na twitter na martani ga wannan takarda mai shafuka 64, shugabar gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya ce, “Manufarmu ba ita ce a yanke alaƙa da birnin Beijing ba. Amma muna son rage dogaro da ita a nan gaba.” Yayin da manufar “de-risking” wato “yin taka-tsantsan da haɗarin mu’amala” da ƙasar Sin na iya zama kamar abin sha’awa ga wasu, amma ya zama wajibi a yi la’akari da yadda za a tinkari lamarin ta fuskar diflomasiyya da tattalin arziki, da yiwuwar “abin da zai biyo bayan rabuwar” da kuma “haɗarin yanke hulɗa” da ƙasar Sin wanda bai kamata a yi watsi da su ba”.
Sin ta kasance babbar abokiyar cinikayyar Jamus a cikin shekaru bakwai da suka gabata, lamarin da ya sa su zama masu taka muhimmiyar rawa wajen cin gajiyar tattalin arzikin juna. Hatta wannan takardar “dabaru” da aka wallafa ba tare da zurfafa tunani ba, ta yarda cewa, ƙasar Sin ita ce babbar abokiyar ciniki daya tilo ta Jamus. A cewar ofishin ƙididdiga na Tarayyar Jamus, cinikayya tsakaninsu ta zarce dala biliyan 335.3 a shekarar 2022. Kusan kamfanoni 6,000 na Jamus ne ke gudanar da harkokin kasuwanci a ƙasar Sin wanda ake sa ran zai ƙaru.
Ban da haka kuma, binciken da ƙungiyar ’yan kasuwa ta Jamus ta gudanar ya nuna cewa, kashi 77 cikin 100 na kamfanonin Jamus na da shirin faɗaɗa harkokinsu a ƙasar Sin nan da shekaru biyar masu zuwa. Wannan bayanai na nuni da muhimmancin dangantakar tattalin arziki tsakanin Beijing da Berlin, wadda za ta fuskanci halin kaka-nika-yi saboda wannan gurguwar tunaninsu na “de-risking”.
A sa’i daya kuma, dabarun “de-risking” ya haifar da shakku a tsakanin ’yan kasuwar Jamus kan ko wannan dabarar za ta iya tabbatar da daidaito na rage dogaro da tattalin arzikin ƙasar Sin, ba tare da yin barazana ga dangantakar kasuwanci dake tsakaninsu ba. A gaskiya, rage hulɗar kasuwanci tare da babbar abokiyar cinikayyarta ba tare da kyakkyawan shiri ba, Jamus a zahiri tana sanya wa muradun tattalin arzikinta sarka ne wanda tuni rikicin Ukraine da cutar Covid-19 suka illata, wanda a ƙarshe za ta yi sanadin koma bayan tattalin arzikinta.
A matsayinta na ƙasa ta biyu mafi ƙarfin tattalin arziki a duniya, ƙasar Sin tana da muhimmin matsayi kuma mai ɗorewa a cikin mizanin samar da kayayyaki a duniya. Kamfanonin Jamus da yawa sun kafa masana’antu a ƙasar Sin kuma sun dogara ga masu samar da kayayyaki na ƙasar Sin don tabbatar da daidaiton farashin kayayyaki.
Shawarar da Berlin ta yanke na karkata hajojinta daga Sin za ta kasance mai sarƙaƙƙiya, mai tsada, kuma mai ɗaukar lokaci. Haka kuma, shawarar kau da kai daga ƙasar Sin, za ta kawo cikas ga tsarin samar da kayayyaki a duniya, wanda zai haifar da ƙaruwar farashin kayayyaki ga masu zuba jari na Jamus.
Sin tana alfahari da masu cin kasuwarta da suka zarta biliyan. Yawan mabuƙatan kayan masarufi masu matsakaicin kuɗin shiga dake cin kasuwan Sin na ƙara bunƙasa kasuwar. Da irin wannan hada-hadar, kasuwar Sin ta kasance babbar dama ga Jamus wacce take neman bunƙasuwa ga hajojinta. Tun da wannan dabarar tasu ta “de-risking” na nufin taƙaita yin mu’amala da Sin, to kasar Jamus ce za ta yi hasarar wannan babbar damar ta cin kasuwar Sin.
Ƙasar Sin tana da kwararrun ma’aikata masu himma da kwazo waɗanda suka taka rawa wajen ba da gudummawar da Sin ta samu a matsayin babbar cibiyar tattalin arziki a duniya. Abin lura shi ne, kamfanonin Jamus suna sha’awar Sin saboda saukin kuɗin kwadago. Wannan dabarar tasu ta “a raba gari” za ta yi illa ga ’yan kasuwa na Jamus da suka dogara ga kwararrun ma’aikata na ƙasar Sin, ko kuma ba da wani bangare na ayyukansu ga ƙasar Sin, za su fuskanci matsaloli wajen neman ƙarin kwararrun ma’aikata a farashi mai rahusa.
Kasancewar ƙasar Sin, babbar tattalin arziki a Asiya, da Jamus, babbar tattalin arziki ta EU, suna ɗauke da nauyin da ya rataya a wuyansu na haɗin gwiwa wajen tinkarar ƙalubalen da duniya ke fuskanta tare da tabbatar da zaman lafiya da wadata. Ta fuskar wadannan nauyin dake rataya a wuyansu, kamata ya yi Berlin ta ɗauki Beijing a matsayin abokiyar hulɗar da ba ta da makawa wajen tinkarar ƙalubalen duniya, ba abokiyar gaba ba.
Babu shakka, nesantar ƙasar Sin ba zato ba tsammani, zai ƙara ta’azzara rashin imani da rashin fahimtar juna, ya kamata Jamus ta yi la’akari da wadannan dalilai domin farfado da tattalin arzikin duniya da tabbatar da zaman lafiyar duniya. (Yahaya Babs)