Kasar Argentina tana daya daga cikin kasashen mafiya nisa da kasar Sin a fadin duniya. Kasar na da albarkatun amfanin gona da dabbobi, amma, tana fama da matsalar yadda za ta iya sayar da hatsi da naman da take da su zuwa kasuwannin kasashen ketare, sakamakon koma bayan sufurin layin dogo.
Layin dogo na Belgrano, wanda aka gina a shekara ta 1876, wata muhimmin layin dogo ne da ta shafi yankunan da ake noman amfanin gona na kasar Argentina, sai dai saboda rashin gyara, an yi watsi da kusa kilomita dubu 7 na layin, kuma daruruwan kilomita kacal suke aiki.
- Sin Za Ta Fadada Girman Tashar Binciken Samaniyarta
- “Makon Zinare” Ya Kore Surutan Tabarbarewar Tattalin Arzikin Kasar Sin
A watan Yulin shekarar 2014, shugabann kasar Sin Xi Jinping, wanda ya ziyarci kasar Argentina a karon farko, ya shaida bikin bude aikin sake gina layin dogo na Belgrano a ranar da ya isa kasar. Wannan muhimmin shiri ne da kasar Sin da Argentina suka kulla bisa shawarar “Ziri daya da hanya daya”.
A watan Yuni na shekarar 2023, an kammala kashin farko na aikin gyara layin dogon Belgrano cikin nasara, wannan layin dogo ya hada yankunan da ake noma amfanin gona da tashar jiragen ruwa na kasar Argentina, wanda ya sa aka cimma nasarar rage lokacin sufurin hajoji tsakanin yankin da ake noma amfanin gona zuwa tashar jiragen ruwa daga kwanaki uku zuwa kwana daya, ya kuma samar da guraben ayyukan yi sama da 4800 ga al’ummomin dake zaune a wuraren kusa da wannan layin dogo.
A watan Fabrairu na shekarar 2022, kasar Sin da kasar Argentina sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna game da shawarar “Ziri daya da hanya daya”. A halin yanzu, an shigar da karin naman sa da ’ya’yan itatuwa da kuma amfanin teku daga kasar Argentina zuwa kasuwannin kasar Sin. Kana, kasar Sin ta kasance daya daga cikin muhimman abokan ciniki na kasar Argentina, kuma, kasar da ta fi shigar da amfanin gona daga kasar Argentina. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)