Bisa kididdigar da kamfanin layin dogo na kasar Sin ya fitar, daga fara zirga-zirgar hutun ranar ma’aikata a ranar 29 ga Afrilu zuwa ranar 4 ga Mayu, jiragen kasa na kasar Sin sun yi jigilar fasinjoji miliyan 112, adadin da ya karu da kashi 10.5 cikin dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin a bara, tare da tabbatar da zirga-zirga cikin aminci, kwanciyar hankali da kuma tsari. A yau, yawan fasinjojin da ke kan hanyarsu ta dawowa daga hutun ta jiragen kasa na ci gaba da karuwa, inda a yau ake sa ran za a yi jigilar fasinjoji miliyan 21.1 ta hanyar jirgin kasa na kasar, yayin da ake shirin kara jiragen kasan fasinja 1896 a kan adadin jiragen da ake amfani da su a baya wajen jigilar fasinjoji. (Mai fassara: Mohammed Yahaya)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp