A wasu hare-haren jiragen yakin sojojin saman Nijeriya, NAF da suka kai, sun yi nasarar tarwatsa ma’ajiyar abinci na ‘yan ta’adda tare da kashe wasu da dama a yankin tafkin Chadi.
A wata sanarwa da kakakin rundunar NAF, Air Cadre Olusola Akinboyewa, ya fitar, ya ce rundunar sojin saman ‘Operation Hadin Kai’ (AC OPHK) ce ta aiwatar da harin a ranar Asabar, 23 ga watan Nuwamba, 2024, a yankin Jubillaram, wanda ya yi kaurin suna a cikin yankin Tumbuns na tafkin Chadi.
- Ra’ayin Matasa Kan Kungiyar ‘Yan Ta’adda Mai Suna Lakurawa Da Ta Fito A Kebbi
- Leicester City Ta Kori Kocinta Bayan Rashin Nasara A Hannun Chelsea
Ya ce, wurin da aka gano, wanda aka gano ta hanyar bincike mai zurfi, ya kasance wurin da ake ajiye abinci mai muhimmanci da kuma mafaka ga kwamandojin ‘yan ta’adda da mayakansu.
A cewar sanarwar, bayanan sirri sun danganta ayyuka tare da zirga-zirgar ‘yan ta’adda a wurin bayan hare-haren baya-bayan nan, ciki har da harin da aka kai wa sojoji a Kareto a ranar 16 ga Nuwamba, 2024.
Akinboyewa ya kuma ba da tabbacin cewa, NAF za ta ci gaba da gudanar da hare-harenta tare da na hadin gwiwa har sai an murkushe ‘yan ta’adda da barazanar su a Nijeriya.