Akalla manyan shugabannin ‘yan ta’adda uku; Abu Asad, Ibrahim Nakeeb, Mujaheed Dimtu, Mustafa Munzir da mayaka sama da 100 sojojin saman Nijeriya suka kai kashe a yakin Tagoshe da ke tsaunin Mandara a Jihar Borno.
Daraktan hulda da jama’a da yada labaran rundunar sojin saman (DOPRI), a wata sanarwa, ya ce harin da aka kai a ranar 24 ga watan Nuwamban 2023 sun yi nasara lalata gine-ginen ‘yan ta’adda.
- Za A Yi Gwanjon Rigunan Messi Na Gasar Kofin Duniya Ta 2022 Da Kudi Tsagwagwa
- Firaministan Kasar Sin Ya Gana Da Ministar Harkokin Wajen Faransa
Ya ce sun hangi ‘yan ta’adda a wani inda suka kai samae.
Air Commodore Gabkwet ya ce, “Daga bidiyon da muka gani mun hangi ‘yan ta’addan na taruwa a wani waje.
Ya kara da cewa, “Sama da ‘yan ta’adda 100 dauke da muggan makamai muka gani.
“Bayan harin da aka kai ta sama an lalata musu kayayyaki da gine-gine da makamai.
“Haka kuma an samun alamun cewa Abu Asad, jigo a kungiyar Ali Ngulde a karkashin Boko Haram, da kuma sauran ‘yan ta’adda kamar Ibrahim Nakeeb, Mujaheed Dimtu, Mustafa Munzir da mayaka da dama na daga cikin ‘yan ta’addan da aka kashe a harin ta sama”.
Shugaban Rundunar Sojan Sama, Air Marshal Hasan Abubakar ya yaba wa Kwamandan Rundunar Sojojin Sama da mutanensa.
Ya kuma bukace su da su ci gaba da hada hannu da rundunar sojin kasa yayin gudanar da ayyukansu.