Hukumar Alhazai ta Nijeriya, ta kammala jigilar maniyyata aikin hajjin bana na shekarar 2024, zuwa Ƙasar Saudiyya, yayin da jirgin ƙarshe ya sauka a filin jirgin saman Yarima Mohammed bin AbdulAziz, da ke Madina da yammacin yau Litinin.
Jirgin ya ɗauki sauran maniyyata 211, daga birnin tarayya Abuja da jihohin Zamfara da Sokoto da Kebbi da Bauchi da Niger da kuma wasu jami’ai, wanda hakan ya kawo ƙarshen jigilar maniyyata na shekarar 2024 zuwa Makkah.
- Maniyyata Hajji Biyu Daga Kwara Sun Mutu
- Hajjin 2024: Wani Alhaji Dan Nijeriya Daga Jihar Kebbi Ya Rasu A Makkah
Hakan tabbaci ne na kammala jigilar maniyyatan sa’o’i 72 kafin cikar wa’adin ƙarshe na rufe saukar maniyyata daga ƙasashen duniya da mahukuntan Saudiyya suka ƙayyade na kakar bana, inda Hukumar NAHCON ta samu nasarar kammala jigilar maniyyatan Nijeriya ɗari bisa ɗari zuwa Madina kafin ranar Arafat.