Fara jigilar fasinjoji akan layin dogo na jihar Legas wanda aka fi sani da ‘Red Line’ ya fara aiki a yau Talata 15 ga watan Oktoba bayan da gwamna Babajide Sanwo-Olu ya kaddamar da shi a hukumance.
Da yake magana kan aikin, gwamnan ya ce, wannan shi ne tsarin layin dogo na biyu da zai fara aiki cikin kasa da shekaru biyu a jihar, inda ya roki ‘yan Legas da su kara kulawa da irin wadannan ababen more rayuwar da ke jiharsu.
- Yadda Ake Kula Da Jama’a Ya Fi Muhimmanci
- Gwamnatin Sakkwato Ta Kafa Kwamitin Da Zai Fara Sayar Da Kayan Abinci Masu Sauki
Layin dogo na ‘Red Line’ mai tsawon kilomita 27 yana da tashoshi takwas da suka hada da Oyingbo, Yaba, Mushin, Oshodi, Ikeja, Agege, Iju, da Agbado a jihar Legas.
An yi hasashen cewa, jirgin zai jigilar fasinjoji kusan 500,000 kowace rana.