Aƙalla mutane biyu ne suka rasu a ranar Laraba lokacin da wani jirgin ƙasa ya murƙushe adaidaita sahu a yankin Phototech, a ƙaramar hukumar Jos ta Kudu, a Jihar Filato.
Jirgin ya taso ne daga Bukuru zuwa tsakiyar birnin Jos lokacin da hatsarin ya auku.
- Dantsoho Ya Nemi Hadin Kan Kasashen Afrika Wajen Bunkasa Tashoshin Jiragen Ruwa
- Majalisa Ta Nuna Damuwa Kan Rahoton Yiwuwar Asarar Dala Biliyan 300 A Badaƙalar Ɗanyen Mai
Shaidu sun ce hatsarin ya auku ne da misalin ƙarfe 11 na safe lokacin da direban adaidaita sahun ya yi ƙoƙarin ƙetare titin jirgin ƙasan alhali jirgin ya taho a guje.
Jirgin ya yi awon gaba da adaidaita sahun nan take, inda direban da wani fasinja suka rasu a nan take. Wasu mata biyu da ke cikin adaidaita sahun sun jikkata sosai, kuma aka garzaya da su asibiti
Wani mutum mai suna Muhammad Ibrahim ya ce hatsarin ya firgita jama’ar da ke wajen.
Ya ce, “Direban ya yi ƙoƙarin ketare titin kafin jirgin ya wuce, amma lokaci ya ƙure. Da ƙarfi ya yi awon gaba da shi, adaidaita sahun ya tarwatse gaba ɗaya.”
Mai magana da yawun tashar jirgin ƙasa ta Jos, Adam Abdullahi, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya bayyana cewa direban ya ƙi bin umarnin jami’in tsaro na titin jirgin.
Ya ce, “Jami’inmu a wajen ya nuna masa alamar tsayawa, amma ya ƙi tsayawa. Gudun jirgin kada ya cimma masa, hakan ya haddasa hatsarin.”
Abdullahi ya yi gargaɗi direbobi da masu adaidaita sahu da su riƙa bin dokokin titin jirgin ƙasa, tare da tsayawa idan jirgi ya taho.
Ya ce hukumar jiragen ƙasa za ta ci gaba da wayar da kan jama’a domin gujewa irin wannan mummunan lamari a nan gaba.
Wasu mazauna yankin sun roƙi gwamnati da ta sanya ƙarin alamomin gargaɗi da shinge a wuraren da titin jirgin ƙasa ke wucewa domin hana sake faruwar irin wannan hatsari.
Sannan sun buƙaci direbobi da su riƙa yin taka-tsantsan yayin kusantar titin jirgin ƙasa.














