Jirgin Ruwan farko makare da alkama daga Ukraine ya isa gabar ruwan Turkiya, jami’an tashar jiragen ruwan sun tantance jirgin don tabbatar da abinda jirgin ya dauko.
Hakanna zuwa ne karkashin wata yarjejeniyar sulhu da ke son ganin Rasha ta janye sojojin ruwanta daga hanyar da ta datse ta tekun Black Sea.
Jirgin wanda ya tashi karkashin wata yarjejeniyar da aka cimma tsakanin majalisar dinkin duniya da Turkiya da zummar fitar da dimbim tan-tan na hatsi da suka makale a Ukraine don magance matsalar karancin abinci da ta kunno kai a duniya, a safiyar yau ne ya isa Istanbul dauke da tutar Sierra Leone.
Jirgin ya isa gabar ruwan Bosphorus Strait ne jim kadan bayan da Ukraine ta sanar da fara kwashe fararen hula daga yankin Donetsk da ke shan luguden wuta ba kakkautawa daga Rasha, wanda ke matsayin irinsa na farko cikin watanni 5 da ya iso gabar ruwan daga Ukraine bayan fara mamayar Moscow.
Matakin Rashan na sanya sojoji akan ruwa da ya hana fitar da hatsi daga Ukraine ya jefa duniya a halin kunci da yunwa saboda karanci da kuma tsadar abincin da ake fuskanta a watanni 5 da suka gabata.
Rfi Hausa