Wani jirgin saman rundunar sojojin saman Nijeriya, NAF ya yi nasarar tarwatsa wani shahararren dan ta’adda Boderi da mayakansa a maboyarsu da ke Tsauni Doka a karamar hukumar Igabi ta jihar Kaduna.
A wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a da yada labarai na NAF (DOPRI), Air Cdre Edward Gabkwet, ya fitar, ta ce, bayan samun bayanan sirri kan bayyanar shugaban ‘yan ta’addan da aka fi sani da Boderi tare da mayakansa a Tsauni Doka, nan take Jirgin ya ta shi don tarwatsa ‘yan ta’addan da maboyarsu.
- Dan Majalisar Amurka Ya Yi Wa Takwaransa Mahangurba
- Wace Hanya Yankin Asiya Da Pasifik Zai Bi Don Sake Kirkiro Al’ajabi A Shekaru 30 Masu Zuwa?
Sanarwar ta ce, an aka kai harin ne ta sama da sanyin safiyar ranar 16 ga watan Nuwamba, 2023, inda aka yi wa ‘yan ta’addan mummunar illa.
Sanarwar ta ce, an kuma kai hare-hare makamancin wannan a wani wuri mai tazarar mita 500 gabas da maboyar Boderi, wanda ake kyautata zaton maboyar dan uwan Boderi ne, wanda akafi sani da Nasiru.
Ya ce: “Dukkanin hare-haren biyu an yi nasara sosai sabida an kashe ‘yan ta’adda da dama tare da lalata baburansu.”
Ya ce Boderi da dan uwansa Nasiru, tare da mayakansu, suna da hannu wajen kai munanan hare-hare da kuma sace-sacen mutane a hanyar Abuja zuwa Kaduna, hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari da kuma wasu al’ummomi a jihohin Neja da Kaduna.