Rundunar Sojin Sama da rundunar sojin kasa na sojojin Nijeriya, a ranar 30 ga watan Junairu, 2024, sun kashe ‘yan ta’adda da dama tare da lalata maboyarsu a jihar Katsina.
Daraktan hulda da jama’a da yada labarai (DOPRI) na rundunar sojin sama, Air Vice Marshal Edward Gabkwet, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce hadin gwiwar ta yi sanadin kawar da ‘yan ta’adda da dama tare da lalata maboyarsu da ke kan tsaunin Tora a Karamar Hukumar Safana ta Jihar Katsina.
Ya ce, jirgin rundunar sojin saman (NAF) ne ya fara kai wa maboyar hari, inda daga nan sojojin kasa suka yi nasarar kashe sauran ‘yan ta’addan da suka tsere.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp