Hamshakin dan kasuwa dan kasar Afrika ta kudu, Johann Rupert, mai shekaru 73 ya doke fitaccen attajirin nan dan Nijeriya, Aliko Dangote, a matsayin wanda ya fi kowa kudi a Nahiyar Afirka.
Johann Rupert, wanda aka kiyasta darajar dukiyarsa ta kai dala biliyan 12, Mujallar Forbes ta bayyana shi cikin hamshakan attajiran duniya, yayin da Dangote ke biye da shi da dala biliyan 10.8.
Rahotanni sun bayyana cewa darajar Dangote ta yi kasa kan faduwar darajar Naira a sakamakon matakin da babban bankin Nijeriya ya dauka na yin gwanjon dala a farashi mai rahusa fiye da farashin kasuwa.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp