ADVERTISEMENT
  • English
  • Business News
Friday, July 17, 2026
Leadership Hausa
Read English News
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
  • Gida
  • LabaraiZafi
    • Kananan Labarai
    • Daga Kasar Sin
    • Dausayin Musulunci
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Manyan Labarai
    • Ado Da Kwalliya
    • Bakon Marubuci
  • Wasanni
  • Siyasa
  • Labaran Kasuwanci
  • Daga Birnin Sin
  • Nishadi
  • Ra’ayi Riga
  • Taskira
  • Al’ajabi
  • Al’adu
No Result
View All Result
Leadership Hausa
No Result
View All Result

Alfanun Katafariyar Matatar Man Dangote Ga Nijeriya

by Abubakar Abba
3 years ago
Dangote

Sabuwar matatar man dangote da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya kaddamar a farkon makon nan za ta kasance mai matukar alfanu ba ma kawai ga Nijeriya ba har da yankin Afirka baki daya. Kadan daga ciki shi ne yadda matatar za ta taimaka wa Nijeriya ceto dalar Amurka biliyan 30 da take kashewa wajen tace mai daga kasashen waje, tare da habaka shigo da kudaden kasashen waje akalla Dala biliyan 10.

Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da sauran shugabannin Afirka biyar suka ba da tabbacin Afirka za ta samu sa’ida wajen zuwa kasashen turawa sayo tataccen mai da kuma bunkasa hada-hadar kasuwanci. Shi kansa Shugaba Muhammadu Buhari ya ce matatar za ta taimaka wajen ciyar da Nijeriya gaba ta fuskar dogaro da kai da samar da abinci, da dai sauran muradun kasa.

  • Sin Ta Bukaci A Tallafawa AU Kan Aikin Wanzar Da Zaman Lafiya

Da yake jawabi a wurin kaddamar da rukunin matatar man ta Dangote da ke Legas a ranar Litinin, 22 ga watan Mayu, 2023, gwamnan babban bankin CBN, Godwin Emefiele, ya bayyana cewa matatar Dangote da ke da karfin sarrafa gangar danyen mai 650,000 a kowace rana ita ce matatar mai mafi girma a duniya kuma za ta kara habaka samun kudaden waje wanda zai kara karfafa asusun ajiyar gwamnati da kuma daidaita farashin kudaden musaya.

ADVERTISEMENT

Ya lura cewa, ana sa ran tasirin ajiyar zai fito fili baro-baro a cikin asusun ajiyar Nijeriya na waje ta hanyar rage matsin lamba kan ma’aunin biyan kudi, yana mai cewa “har ila yau akwai fa’idodi masu yawa da za mu samu daga fitar da kayan da matatar za ta rika sarrafawa tana fitawar zuwa sauran duniya.

“Bugu da kari matatar man za ta taimaka wa Nijeriya wajen tsumin dalar Amurka biliyan 30 da ake kashewa wajen shigo da man fetur, sannan ana hasashen tattalin arzikin kasar zai amfana da karin dalar Amurka biliyan 10 na kudaden musaya a duk shekara ta hanyar fitar da tataccen man fetur zuwa kasashen waje, wanda hakan zai kara habaka asusun ajiyarmu a hukumance da saukaka wahlhalun da ake sha na musayar musayar kudi.

LABARAI MASU NASABA

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

“Wannan aikin zai kuma ba da tallafi ga ayyukan kasafin kudi na gwamnati kamar yadda zai taimaka wajen saukaka matsalolin makudan kudin da ake warewa a kan tallafin man fetur da kuma samar da tanadin kasafin kudi mai inganci. Bayanai da ake samu sun nuna cewa, a cikin shekaru biyar, tallafin man fetur a Nijeriya ya haura sama da ninki tara daga kimanin Naira biliyan 154 a shekarar 2017 zuwa sama da Naira Tiriliyan 1.43, kafin ya kuma tashi zuwa Naira Tiriliyan 4.4 a karshen shekarar 2022.

“Hasashen na nuna cewa wannan adadi zai iya zarce Naira tiriliyan 7 a cikin shekaru uku masu zuwa idan ba mu magance shi yadda ya kamata ba. Alhamdu lillahi, matatar mai ta Dangote za ta iya ceto wa Nijeriya kimanin Naira Tiriliyan 5 zuwa Naira Tiriliyan 7 a duk shekara a cikin kasafin kudin Gwamnatin Tarayya nan da shekaru biyar masu zuwa,” in ji shi.

A halin da ake ciki, Emefiele ya bayyana cewa, rukunin Dangote ya fara biyan wasu lamunin kasuwanci tun kafin kaddamar da wannan cibiyar wanda ya ce yana nuna iya kasuwancin kamfanin da shugabansa. Bayan biyan wani kaso mai yawa, basusuka sun ragu sosai daga sama da dala biliyan 9 zuwa dala biliyan 3.

“A daidai wannan lokaci dole ne in yaba wa dukkan bankunan Nijeriya da ke cikin gida, wadanda ba wai kawai sun hada hannu da aikin ta hanyar samar da kudade masu inganci ba, amma suna da masaniya kan muhimmancin aikin ga al’ummarmu. Sun ba da tallafi mai yawa da fahimta ta musamman, hatta lokacin biyan kudin ruwa da adadin abin da za a rika biya sun ragu sosai,” in ji shi.

A nasa jawabin, shugaba Buhari, ya ce matatar man Dangote ta kara nuna jajircewar Alhaji Aliko Dangote, inda ya kara da cewa kamfanin zai ciyar da Nijeriya gaba wajen dogaro da kai wajen samar da abinci, da dai sauran muradun kasa.

A cewarsa, matatar mai ta Dangote da ke zama matatar mai mafi girma a Nahiyar Afirka, tare da masana’antar takin zamani, za ta taimaka wa ‘yan Nijeriya wajen aikin noma a matsayin sana’a ta ainihi da ake cin gajiyarta koyaushe da kuma bayar da gudunmawa wajen daidaita harkar man fetur a kasar.

Dangote
Abubakar Abba
+ postsBio
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Dalilin Da Ya Sa Kungiyar NCTR Ta Jinjina Wa Shugaban NPA
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Nazari A Kan Wasu Cututtuka Da Ke Shafar Dabbobi Lokacin Damina
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Sharhi A Kan Dabarun Zamani Na Yin Auren Ƴaƴan Itatuwa
  • Abubakar Abba
    https://hausa.leadership.ng/author/abubakar-abba/
    Ɗantsoho Ya Jinjina Wa Hukumar FCC Kan Sabbin Sauye-Sauyen Da Ta Samar

MASU ALAKA

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau
Rahotonni

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

July 17, 2026
Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara
Rahotonni

Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

July 17, 2026
Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya
Rahotonni

Na Yi Tsayin-daka Domin Cika Alƙawarin Ƙasata Nijeriya

July 14, 2026
Next Post
Xi Jinping Na Fatan Sin Da Janhuriyar Dimokuradiyyar Congo Za Su Yi Aiki Tare Wajen Bunkasa Ci Gaba Da Samar Da Makoma Ta Gari

Xi Jinping Na Fatan Sin Da Janhuriyar Dimokuradiyyar Congo Za Su Yi Aiki Tare Wajen Bunkasa Ci Gaba Da Samar Da Makoma Ta Gari

LABARAI MASU NASABA

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

Wasu Sassan Birnin Abuja Na Fuskantar Barazanar Rusau

July 17, 2026
Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

Mata Manoma Sun Gina Gada, Rijiyar Burtsatse A Danbare, Kano

July 17, 2026
Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

Yadda NDLEA Ke Fatattakar Dillalan Miyagun Kwayoyi Na Kudancin Amurka

July 17, 2026
Gwamnan Da Bai Taba Samun Mulkin Jihar Kano Ba

Gwamnan Da Bai Taba Samun Mulkin Jihar Kano Ba

July 17, 2026
An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

An Ceto Wasu Mutane Huɗu Da Aka Sace A Kogi

July 17, 2026
NPA Ta Tara Kudin Shiga Naira Biliyan 758.2 A 2024

Dalilin Da Ya Sa Kungiyar NCTR Ta Jinjina Wa Shugaban NPA

July 17, 2026
Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

Yunkurin Dauda Lawal Na Bunkasa Bangaren Ma’adanan Jihar Zamfara

July 17, 2026
Gbajabiamila Ya Maka Daraktan Bogi Na PFIPC Kotu, Ya Nemi Diyyar Biliyan 15

Gbajabiamila Ya Maka Daraktan Bogi Na PFIPC Kotu, Ya Nemi Diyyar Biliyan 15

July 17, 2026
Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

Bayan Ceto Daliban Oyo: Kallo Ya Koma Borno Da Yobe

July 17, 2026
Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

Batun Yawan Bashin Da Nijeriya Ke Ciyowa Daga Ketare

July 17, 2026

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
    • Manyan Labarai
    • Kananan Labarai
    • Masarautu
    • Bakon Marubuci
    • Dausayin Musulunci
    • Daga Kasar Sin
    • Nishadi
    • Noma Da Kiwo
    • Sana’a Sa’a
    • Tambarin Dimokuradiyya
    • Taskira
    • Daga Birnin Sin
    • Ado Da Kwalliya
  • Siyasa
  • Wasanni
  • Al’adu
  • Al’ajabi
  • Labaran Kasuwanci
  • Karanta cikin Turanci

© 2025 Leadership Media Group - All Right Reserved.