Mataimakin shugaban kwamitin shirya gasar Olympics ta kasa da kasa Juan Antonio Samaranch Jr. ya ce, shugaban kasar Sin Xi Jinping, muhimmin abokin tafiya a fannin tabbatar da nasarar gasannin Olympics na kasa da kasa.
Mista Samaranch Jr. wanda ya bayyana hakan a jiya Litinin, yayin wata tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua a birnin Hangzhou, a gefen gasar wasanni ta Asiya karo na 19 dake gudana yanzu haka. Ya ci gaba da cewa, himmar shugaba Xi, da tallafinsa ga harkokin wasa, da irin rawar da gasannin Olympics ke takawa ga rayuwar matasa, da ma daukacin al’umma, suna da matukar muhimmanci.
Jami’in ya kara da cewa, “Abu ne mai faranta rai samun irin wannan muhimmin abokin hulda a fannin wasanni, da harkokin da suka jibanci gasar Olympic ta kasa da kasa.” (Mai Fassarawa: Saminu Alhassan)
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp