Kungiyar kwallon kafa ta Real Balladolid ta zargi Manchester City da karfafa gwiwa ga daya daga cikin ‘yan wasanta, Juma Bah domin ya soke yarjejeniyarsa ya koma buga Premier League da buga wasa. Dan wasan mai tsaron baya, ya sanar da kungiyar ta Sifaniya ranar Talata cewar yana so ya katse yarjejeniyarsa, saboda ya koma Manchester City kan kankanin kudi.
Tun a baya Manchester City ta nemi izinin Balladolid, domin tattaunawa kan sayen matashin mai shekara 18, domin ya koma buga mata wasa amma sai kungiyar ta ce tana son dan wasanta kuma ba na sayarwa bane. Bah bai halarci atisaye ba ranar Laraba ba, inda hukumar kwallon kafar Sifaniya ta tabbatar cewar ya biya sauran kunshin kwantiraginsa a kungiyar, domin ya kara gaba.
Balladolid ta ce matakin da matashin ya dauka Manchester City ce da wakilin dan wasan suka kitsa komai, ta kuma yi Alla-wadai da wannan lamarin. Dan wasan mai shekara 18 ya koma kungiyar kwallon kafa ta Balladolid daga AIK Freetong, domin buga wasannin aro a bara, inda a watan nan Balladolid ta mallaki dan wasan bayan ya yi kokari kuma ya burge masu koyar da kungiyar. Sai dai Bah yana kan tsarin yarjejeniya ta matashin dan wasa, amma bai amince ya saka hannu ba kan kwantiragi a matakin kwararren dan wasa ba.
Balladolid ta ce za ta dauki mataki na shari’a kan Bah, za kuma ta yi dukkan abin da ya kamata domin ta kare martabarta amma kuma har yanzu kungiyar kwallon kafa ta Manchester City ba ga ce komai ba a kan zargin da ake mata na hurewa Bah kunne