Majalisar Dattawan Nijeriya ta sake jaddada gargaɗinta ga sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya da aka dakatar, Natasha Akpoti-Uduaghan, da ta nisanci harabar Majalisar Tarayya, ta ce babu wani hukuncin kotu da ya tilasta dawo wa da ita majalisar.
Wannan sabon gargaɗi ya biyo bayan sanarwar da Akpoti-Uduaghan ta yi a ranar Asabar cewa za ta koma majalisar a ranar Talata, 22 ga Yuli, bisa hukuncin da babbar kotun tarayya da ke Abuja, ƙarƙashin Mai Shari’a Binta Nyako ta yanke kwanan nan.
- Ba Zamu Dawo Da Sanata Natasha Zauren Majalisa Ba, Sai Mun Karɓi Kwafin Hukuncin Kotu – Majalisa
- Sanata Natasha Ta Bayyana Dalilin Da Ya Sa Ba Ta Koma Majalisa Ba
A martani da shugaban kwamitin yaɗa labarai na majalisar dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya fitar a ranar Lahadi, ya ƙaryata ikirarin sanatar, yana mai cewa kotun ta bayar da shawara ne, ba da umarnin dole ba, ga majalisar dattawa.
“A karo na uku, majalisar dattawa ta sake jaddada cewa babu wani hukuncin kotu da ya tilasta mayar da Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan kafin lokacin dakatarwarta ya ƙare,” cewar Adaramodu.
Ya bayyana cewa hukuncin kotun ya bayar da shawa ne kawai kan a duba tsarin dokokin majalisar da yiwuwar sake bitar hukuncin dakatarwar, wanda kotun ta bayyana yana iya zama mai tsauri.
Ya kuma jaddada cewa kotun ta tabbatar cewa majalisar ba ta karya doka ko kundin tsarin mulki ba a yanke wannan hukunci.
“A maimakon bayar da umarnin dole, kotun ta bayar da shawara ne,” in ji shi. “Har ila yau, kotun ta same ta da laifin raina kotu, ta ci ta tara ₦5 miliyan tare da umarnin bayar da haƙuri a manyan jaridu biyu da kuma shafinta na Facebook. Waɗannan umarni ba a cika su ba har yanzu.”
Ya gargadi Natasha cewa duk wani yunƙuri na dawo wa ta karfi ta hanyar amfani da fassarar da ba ta dace da hukuncin kotu ba, zai zama tauye doka da raina hurumin majalisa.
“Majalisar na jaddada cewa babu wani umarni na dole da ke tilasta dawowarta,” in ji shi. “Za mu yi nazari kan shawarar kotu a lokacin da ya dace, kuma za mu sanar da matakin da aka ɗauka.”
Majalisar ta buƙaci Natasha da ta girmama tsarin dokokin majalisa, kuma ta kaucewa harabar zauren.
“Ya kamata ta bari tsarin doka ya yi aikinsa,” cewar Adaramodu.
Daga kanmu, magana ta ƙare. Kuna iya samun rahotanni da ɗumi-ɗuminsu da gamsassun ruwayoyin labarai daban da na saura kai-tsaye cikin wayoyinku. Shiga zaurenmu na WhatsApp don sanin halin da ake ciki a duniya ko yaushe
Shiga zaurenmu na WhatsApp