Gwamnatin Tarayya ta fara sayar wa ‘yan jarida buhun shinkafa mai rahusa a Jihar Kaduna, a kan kudi Naira 40,000 kan kowane buhu mai nauyin kilogiram 50, domin rage tsadar kayan abinci.
An ware wa ‘yan jarida buhuna 149, inda kowane ya samu damar sayen buhu guda daya.
Hukumar EFCC da Ma’aikatar Noma sun tantance masu siyan shinkafar don tabbatar da gaskiya.
Ma’aikatan gwamnati kuma sun karbi nasu a wuraren aikinsu.
Shugabar NUJ reshen Kaduna, Hajiya Asma’u Halilu, ta yaba wa gwamnati kan wannan tsari, tare da rokon a ci gaba da shirin don bai wa wasu dama su amfana.
Ministan Noma, Sanata Abubakar Kyari, ya bayyana cewa shugaba Bola Tinubu ne, ya bayar da umarnin wannan mataki don yakar yunwa da rage tsadar kayan abinci.
Ya ce shigo da tan 30,000 na shinkafa kasuwa zai taimaka wajen rage farashin kayan abinci tare da amfanar ‘yan Nijeriya.